Gwamnan Neja ya gana da daliban Tegina 91 bayan kwanaki 88 da sukayi hannun yan bindiga
- Daliban Tegina sun dira gidan gwamnan jihar Neja don ganawa da Gwamna
- An sanya musu sabbin kaya kuma Likitoci sun duba lafiyarsu, gwamnan yace
- Mutum daya cikin dalibai 91 ya rasa ransa hannun yan bindigan
Minna, Neja - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya gana da daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko, dake Tegina, kuma an mikasu ga iyayensu.
Ya hadu da su ne a gidan gwamnatin jihar dake Minna, babbar birnin jihar, Sakataren yada labaransa, Mary Noel-Berje, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki.
Gwamnan ya bayyana cewa yara 91 da wasu mutum biyu aka sace kuma 92 sun dawo. Mutum daya cikin yaran ya rasa rayuwarsa.
Abubakar Bello ya yi takaicin yadda yan bindiga zasu sace kananan yara kuma su ajiyesu na tsawon kwanaki 88.
Yace:
"Wannan na nuna rashin hankalin da wasu ke dashi. Idan ba haka ba, ta yaya zaku sace yaro dan shekara uku kuma ku ajiyeshi fiye da kwanaki 80."
"Wannan ya sa iyaye na shakkan aika yaransu makaranta."
Gwamnan ya kara da cewa an duba lafiyar yaran kuma suna nan kalau illa mutum hudu dake bukatar ganin Likita.
Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace
Sama da dalibai 90 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata.
Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.
‘Yan bindiga sun karbi N68m da sababbin babura kafin su fito da ‘Yan Islamiyyan Tegina
Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa sai da aka kara wa ‘yan bindigan kudin fansa bayan sun ki karbar Naira miliyan 50 da aka kai masu a baya.
‘Yanuwa da iyayen wadannan yara sun yi kokarin kara hada Naira miliyan 30 bayan sun biya Naira miliyan 20 domin a ceto yaran a watan Yuni.
Rahoton yace ko da aka je za a ba ‘yan bindigan kudin, sai suka ce an samu gibin Naira miliyan 4.6, suka cigaba da tsare wadannan kananan yaran.
Daga baya an kira iyayen yaran, an nemi su kawo ragowar Naira miliyan 4.6 da kuma cikon Naira miliyan biyu da aka samu a kudin farko da aka kai.
Asali: Legit.ng