Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar

Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar ta baci a fadin kananan hukumomi 14 dake jihar.

Hakazalika gwamnatin ta kulle dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake dukkan kananan hukumomin jihar.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai garin Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar da dafiyar Laraba inda suka yi awon gaba da daliban makaranta.

A cewar TVCNews, dokar ta bacin zata kama ne daga daga karfe takwas na dare zuwa bakwai na safe.

Rahoton tace:

"A cewar gwamnatin jihar, an dauki wannan mataki ne domin dakile hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar."

Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar
Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel