Yanzu-yanzu: Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura

  • Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da cin kasuwar shanu da ake yi a ko wanne mako a fadin jihar
  • Hakan ya biyo bayan hauhawar fashi da makamai da kuma garkuwa da mutane a jihar, kuma dokar zata fara aiki a ranar 1 ga watan Satumban 2021
  • Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayar da wannan sanarwar ta wata takarda ta ranar Talata

Minna, Niger - Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da cin kasuwar shanu ta kowanne mako a fadin jihar a matsayin hanyar magance hauhawar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Daily Trust ta ruwaito cewa, dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumban 2021.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana wannan sanarwar ne ta wata takarda ta ranar Talata inda ya ce wajibi ne duk wani abin hawa da ke dauke da shanu da zai shiga cikin jihar ya nuna takardar shaida da alamar inda aka siyo shanun da kuma inda za a kai su.

Kara karanta wannan

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura
Asali: Original

Gwamnatin ta hana siyar da man fetur a jarka ko wani abu a gidajen mayuka da kuma harkokin manyan motocin da suke daukar itace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sun hana yawon babura a fadin Minna da kewaye sai dai tsakanin 6am zuwa 6pm, Daily Trust ta wallafa.

Matane ya kara da cewa gwamnati ta hana gidajen mai sayar da duk wasu kayan da suka wuce na N10,000 ga abin hawa a lokaci guda.

Sannan ya umarci duk wasu gidajen mayuka da su kula da ababen hawan da za su dinga zuwa suna dawowa don kara siyayya cikin kankanin lokaci.

An samu bayanai a kan yadda aka dakatar da yawon baburan zai ci gaba kuma ya fadada duk inda aka ga akwai yawan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Wadan nan dokokin sun bullo ne bayan kwana 5 da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin bayar da cikakkiyar kariya ga jiharsa daga ta’addanci bayan yaran Islamiyyar Tegina sun kai masa ziyara har gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

SSG ya ce:

Gwamnati ta na sane da takurar da wadan nan dokokin za su iya janyo wa mutane, amma an shinfida dokokin ne don kariya ga mutanen jihar.”

Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata

A wani labari na daban, Peter Aboki, tsohon mataimakin shugaban makarantar noma, kimiyya da fasaha da ke Lafia, jihar Nasarawa, ya maka tsohon kwamishinan noma, Alanana Otaki a babbar kotun Lafia bisa kwace masa matarsa da yayi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, matar da ake rikici a kan ta, Felicia Aboki, ta kai karar mijin ta kotu ta na bukatar a warware aurensu mai shekaru 18.

A ranar Litinin, lauyan Mr Aboki, Shikama Shyeltu, ya bukaci a dakatar da karar da matar Aboki ta kawo don yanzu haka ana batun ta na da wata alaka duk da ta na da aure da tsohon kwamishinan.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng