Bala Ibn Na’Allah ya bayyana tattaunawa ta karshe da ya yi da ‘Dansa kafin ya mutu

Bala Ibn Na’Allah ya bayyana tattaunawa ta karshe da ya yi da ‘Dansa kafin ya mutu

  • Bala Ibn Na’Allah yana tuno waya ta karshe da ya yi da ‘dansa, Abdulkareem
  • Sa’o’i bayan Sanatan ya yi magana da Abdulkareem Na’Allah ne aka kashe shi
  • Na’Allah ya bada shawara a guji siyasantar da rashin tsaro da ake fama da shi

Kaduna - Bala Ibn Na’Allah wanda yake wakiltar mazabar Kudancin Kebbi a majalisar dattawa, ya yi magana game da mutuwar ‘dansa, Abdulkareem Na'Allah.

Bala Ibn Na’Allah ya na zaman makoki a Kaduna

Jaridar Punch ta rahoto Sanata Bala Ibn Na’Allah yana cewa ya yi waya da ‘dan na sa a ranar Lahadin da za a samu wadanda za su je gidansa su kashe shi.

Bala Ibn Na’Allah yace sun zanta da Abdulkareem Na’Allah a kan batun yadda ake fama da matsalar tsaro a Najeriya ana saura awa takawas ya mutu.

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Sanata Na’Allah ya bada labarin wayar karshe da yayi da Kyaftin Abdulkareem Na’Allah ne da aka je yi masa ta'aziyya.

Shugabannin kungiyar ‘yan jarida da manema labarai ta NUJ ta reshen jihar Kaduna, ta je wajen gaisuwan makoki a ranar Talata, 8 ga watan Agusta, 2021.

Shugabar kungiyar masu tattaro rahoto na reshen jihar Kaduna, Hajiya Asmau Halilu ta jagoranci sauran abokan aikin ta zuwa gidan da ake karbar gaisuwar.

Bala Ibn Na’Allah
Sanata Bala Ibn Na'Allah da Abdulkarim Na'Allah Hoto: www.blueprint.ng
Asali: UGC

Mun yi waya karfe 9:27 na dare

Sanatan yake cewa sun kare maganarsu ne a kan yadda ake fama da rashin tsaro a fadin kasar nan. Blueprint ta rahoto Sanatan yana cewa sun bar wa Allah.

Bayan sa’o’i takwas da yin waya da babban ‘dansa, Ibn Na’Allah ya samu labarin cewa an shiga har gida, an makure Abdulkareem Na’Allah, sai da ya mutu.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU na shirin komawa yajin-aiki kwanan nan, ta ba Gwamnatin Buhari wa’adi

‘Dan majalisar yace bai san cewa a lokacin saura kasa da sa’a takwas ya rage masa a Duniya ba.

“Na yi magana da shi ranar Asabar da karfe 9:27 na dare. Na rantse da Qur’ani, maganar rashin tsaro muka yi. Ashe saura masa kasa da awa takwas a Duniya.”

Shugaban kwamitin na harkar sojojin sama a majalisar dattawan Najeriya ya yi kira ga jama’a su guji siyasantar da matsalar tsaro, a tsaya, ayi karatun ta-natsu.

“Ba yau aka fara fama da matsalar nan ba, akwai bukatar mu fahimci lamarin. Idan ba haka ba, za mu rika sha wa ciwo dabam, wani magani na dabam.”

Gwamnati ta yi magana

Ku na da labari kisan Abdulkarim Na’Allah ya sa Gwamnatin Kaduna ta fitar da jawabi. Kwamishinan cikin gida, Samuel Aruwan ya bayyana abin da ya faru.

Samuel Aruwan yace wasu ne suka shiga gida, suka kashe wannan Bawan Allah. Gwamna Nasir El-Rufai ya aika ta’aziyyarsa, ya kuma nemi jami’an tsaro suyi bincike.

Kara karanta wannan

Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel