Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

  • An kama mutane 10 da ake zargin suna da hannu a sabon harin da aka kai kauyen Yelwa Zangam da ke Jos ta arewa, jihar Filato
  • Gwamnan jihar, Simon Lalong, ya kwatanta lamarin da zalunci inda ya yi kiran taro na gaggawa dake da alaka da tsaron yankin
  • Gwamnan ya bukaci jami’an tsaro da su yi gaggawar ganin sun bi diddigi wurin gano wadanda suka yi kisar da masu daukar nauyi

Jos, Plateau - An kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa
Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Lalong ya fusata a kan lamarin wanda rahotanni daga jami’an tsaro sun nuna cewa shirya su aka yi tsaf sakamakon yadda aka lalata gadar da take kai mutane zuwa kauyen don a hana jami’an tsaro zuwa wurin da aka kai harin,” kamar yadda takardar ta shaida.
Gwamna Lalong ya kara da jan kunnen ‘yan ta’addan, inda ya ce za a bi bayan su, a kama su sannan komin daren dadewa, mulkinsa ba zai taba barin ta’addanci ya ci gaba ba.
Hakazalika, zai yi iyakar kokarin ganin ya dawo da zaman lafiya a jihar, kamar yadda yace.

Sai dai Kakakin hukumar ‘yan sanda, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Daily Trust ta ruwaito yadda wani mazaunin yankin, Yakubu Bagudu yake cewa an kashe fiye da mutane 30 a tsakiyan daren Talata sakamakon farmakin.

Bagudu ya kara bayyana yadda aka kona gawawwakin wasu daga cikin wadanda aka kashe.

Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta yi watsi da kiran da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da takwararsa na Jihar Benue, Samuel Ortom, da wasu kungiyoyi da mutane suka yi na cewa mutane su kare kansu daga 'yan bindiga, rahoton Daily Trust.

Ministan Harkokin 'Yan sanda, Mohammed Dingyadi, yayin jawabin shekara-shekara na ma'aikatarsa karo na biyu a hedkwatar yan sanda a Abuja ya ce gwamnati bata goyon bayan mutane su dauki makamai da kansu.

Sannan, Ministan ya kara da cewa Masari yana da ikon fadin ra'ayinsa kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel