Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

  • Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa dole ne mazauna jihar su yi riga-kafin korona ko kuma ta bullo musu ta bayan gida
  • Gwamnan jihar, Godwin Obaseki ya ce za a hana shiga masallatai, majami'u da bankuna ba tare da shaidar yin riga-kafin ba
  • Kamar yadda ya shaida, tarukan shagulgulan biki za su haramta ga duk wanda bashi da shaidar yin riga-kafin muguwar cutar

Benin City, Edo - Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Ta Yi Nasara, Kotu Ta Umarci Likitoci Su Janye Yajin Aiki

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna
Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Bayanin Obaseki kan matakin da zai dauka

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Muna da nau'ikan riga-kafi biyu, akwai riga-kafin Moderna wanda bamu dade da samu ba, akwai kuma riga-kafin Astrazeneca ga wadanda z asu karba kashi na biyunsu.

A cikin kwanakin karshen makon nan ne jihar Edo ta karba magugunan allurar riga-kafi 76,712, wanda ya hada da allurai 65,016 na Moderna da 11,696 na AstraZeneca.

Kamar yadda yace, gwamnati ba za ta rufe jihar ba amma za ta baiwa rayukan jama'a kariya.

Ya kara da cewa daga watan Satumba, za a haramta shiga taro mai mutane da yawa ga wadanda basu karba riga-kafin cutar ba

Kara karanta wannan

An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa

Daga mako na biyu na watan Satumba, ba za a bar jama'a su shiga majami'u, masallatai, wuraren shagulgulan biki, liyafofi da kuma wuraren cin abinci ba, ba tare da katin shaidar yin riga-kafin ba
Hakazalika, daga mako na biyu na watan Satumba, ba za a bar jama'a su dinga shiga bankuna ba, ba tare da katin shaidar yin riga-kafin cutar korona ba. Don haka duk wanda yake son walwala, yayi riga-kafi kawai.

An kama hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo a cikin coci a Legas

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta kama wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne da ya yi yunkurin fitar da hodar ibliss wato koken da hero*n da ganyen wiwi mai nauyin kilo gram 69.65kg zuwa Birtaniya.

The Cable ta ruwaito cewa mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani coci da ke Legas.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Ya ce an gano wanda ake zargin kuma ake nema ruwa a jallo, Stephen Afam Ikeanyionu, a wani coci da ke unguwar Ojodu a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel