Attajirin dan Najeriya ya gwangwanje sama da mutane 120 da tsabar kudi da kayan abinci

Attajirin dan Najeriya ya gwangwanje sama da mutane 120 da tsabar kudi da kayan abinci

  • Hamshakin attajirin nan na Najeriya Marksman Chinedu Ijiomah ya sanya farin ciki a fuskokin mutane biyo bayan irin karamcin da yayi musu a kwanan nan
  • Dan kasuwan wanda shine shugaban rukunin kamfanin Chinmark ya raba tsabar kudi da kayan abinci ga sama da mutane 120
  • Da yake wallafa hotunan shirin, Marksman ya ce al'umma za ta inganta idan mutane suna taimakon juna

Hamshakin attajirin nan na Najeriya, Marksman Chinedu Ijiomah ya da’da’da zukatan mutane da dama a shafukan sada zumunta yayin da ya yiwa wasu mutane alkhairi.

Marksman ya rarraba kayan tallafi na tsabar kuɗi da kayan abinci ga sama da mutane 120.

Attajirin dan Najeriya ya gwangwanje sama da mutane 120 da tsabar kudi da kayan abinci
Attajirin ya ce abubuwa za su inganta idan mutane suna taimakon juna Hoto: Marksman Chinedu Ijiomah
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya yi a shafin Facebook a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, shugaban Kamfanin Chinmark Group ya bayyana cewa bayar da taimako ga mutane shine mabuɗin inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Hotunan da Marksman ya wallafa sun nuna mutane cike da farin ciki yayin da suka karɓi abubuwan da ya yiwa lakabi da tallafi.

Hadiman dan kasuwar sun kasance tare da shi yayin da yake rarraba buhunan kayan abincin da kansa.

Ya rubuta cewa:

"A safiyar yau mun isar da kayan tallafi ga mutane sama da 120 waɗanda ke dogara ga Allah don neman Taimako !!!!
"Idan muka yi abunda za mu iya wajen taimakon juna, al'umma za ta inganta, mu mutane ne na farko.
"Duk abin da muke da shi Allah ne ya ba mu."

'Yan Najeriya sun yaba da wannan namijin kokarin

Ifytex Morah ta rubuta:

"A koyaushe ina yaba muku sannan a lokaci fuda ina aiki tuƙuru don zama kamar ku a nan gaba, ina son albarkar bayarwa ya riske ni .. Allah ya albarkace ni in albarkaci wasu ijn Amin."

Kara karanta wannan

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan Ibrahim Babangida, kujerun ciki kamar zinare

Chukwunonso Eze ya yi tsokaci:

"Kallon ka ya sa na fara mamakin wani irin mutum ne kai? Gaskiya idan rabin masu hannu da shuni za su iya yin rabin abin da kake yi me muke fadi. Allah ya albarkace ka sosai Yallabai."

Favour Gerald tayi sharhi:

"Idan da Gwamnati a kowane mataki zata iya yin rabin irin wannan aikin, wannan ƙasa zata zama wuri mafi kyau. Allah ya albarkace ka yallabai."

A wani labari na daban, Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar imo, ya yi zargin cewa ‘yan siyasar kasar nan na da hannu dumu-dumu a cikin tabarbarewar lamura da rashin hadin kai a tsakanin al’umman kasar.

Okorocha ya bayyana cewa rashin bawa ‘yan kasa masu kishinta damar mulkar kasar na daya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun karuwar masu son a raba kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng