Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata

Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata

  • Peter Aboki, mataimakin shugaban makarantar koyar da noma, kimiyya da fasaha da ke jihar Nasarawa ya maka tsohon kwamishinan noman, Alanana Otaki a kotu
  • Peter ya kai karar kwamishinan sakamakon kwace masa matarsa, Felicia da tsohon kwamishinan ya yi
  • Dama kuma matar da ake rikicin a kan ta ta maka mijin na ta a kotu tana bukatar a warware aurensu mai shekaru 18

Nasarawa - Peter Aboki, tsohon mataimakin shugaban makarantar noma, kimiyya da fasaha da ke Lafia, jihar Nasarawa, ya maka tsohon kwamishinan noma, Alanana Otaki a babbar kotun Lafia bisa kwace masa matarsa da yayi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, matar da ake rikici a kan ta, Felicia Aboki, ta kai karar mijin ta kotu ta na bukatar a warware aurensu mai shekaru 18.

Kara karanta wannan

Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya

Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata
Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A ranar Litinin, lauyan Mr Aboki, Shikama Shyeltu, ya bukaci a dakatar da karar da matar Aboki ta kawo don yanzu haka ana batun ta na da wata alaka duk da ta na da aure da tsohon kwamishinan.

A bangaren lauyan matar, Mr David Meshi, ya ce yanzu haka ta gaji da aurensu mai shekaru 18, shiyasa ta ke bukatar a warware auren, Daily Nigerian ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi kuma Mr Joseph Agbo, lauyan wanda ake kara, ya ce tsohon kwamishinan bai da hannu dangane da rikicin da ke tsakanin mijin da matarsa.

Bayan sauraron dukkansu, alkalin kotun, Abubakar Lanze, ya daga sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Satumba don cigaba da sauraronsu.

Tun ranar Litinin Gwamna Abdullahi Sule ya kori duk wasu Kwamishinonin jiharsa da sauran ma’aikatan da ya dauka na siyasa.

Kara karanta wannan

Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi

Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa

A wani labari na daban, Sanata Bala Ibn Na'Allah, wanda miyagu suka halaka babban dan shi Abdulkareem a gidan shi da ke Malali jihar Kaduna, ya ce rayuwar dan shi ba ta fi ta kowanne dan Najeriya ba.

A wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, Na'Allah ya bayyana fatansa na cewa ta yuwu mutuwar dan sa ta taka babban rawa wurin shawo kan matsalar tsaron Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Na'Allah wanda baya kasar Najeriya yayin da lamarin ya auku, ya ce wadanda suka kai wa dan sa farmaki ba dauke suke da bindigogi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel