Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna

Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya yi ikirarin cewa jiharsa ta fi kowace jiha zaman lafiya a faɗin Najeriya
  • Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga mutanen jihar a wani ɓangare na bikin murnar cika shekara 30 da kafuwa
  • Yace a jihar Kogi akwai mutane kala daban-daban amma sun haɗa kansu fiye da kowane lokaci a Tarihi

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana jihar da yake jagoranta da wacce tafi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan Bello ya faɗi haka ne a yayin da yake jawabi ga mutanen jihar kai tsaye domin murnar cikar Kogi shekaru 30 da kafuwa.

Yace gwamnatinsa ta ɗauki lamarin tsaro, haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali da matukar muhimmanci.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Matawalle Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Buhari Ta Saka Dokar Ta Baci a Arewacin Najeriya

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Mun gina Kogi kan tubali mai kyau

Bello yace an gida jihar Kogi a kan wasu manyan ginshikai uku, na farko shine toshe duk wata kafa ta handama da babakere da kuɗaɗen al'umma.

Gwamnan ya bayyana sauran ginshikan da kawar da asarar ko batar da kuɗaɗe ta hanyar da bata dake ba, da kuma baiwa dukiyar al'ummar muhimmanci wajen tabbatar da duk wata Naira an yi amfani da ita a inda ya dace yadda kowa yake tsammani.

Kogi ta fi kowace jiha zaman lafiya

A jawabinsa, Gwamnan Kogi yace:

"A halin yanzun babu tantama jihar mu ta fi kowace jiha zaman lafiya a faɗin Najeriya."
"An saka mu a matsayin jiha ta biyu a jerin jihohin da suke cikin zaman lafiya, kuma mu ne na biyu a waɗanda suka fi karancin aikata manyan laifuka."

Kara karanta wannan

Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

"Jihar mu na da al'umma kala daban-daban masu ban-banci, amma hakan ba wani abu bane domin muna da haɗin kai fiye da kowane lokaci a tarihin Kogi."

A wani labarin kuma Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Sanata Ali Ndume, ya kirayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito ya yiwa yan Najeriya jawabi.

Sanatan APC yace bai kamata Buhari ya yi gum da bakinsa a lokacin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel