Louis Odumegwu Ojukwu: Muhimman abubuwa 4 game da biloniyan farko na Najeriya

Louis Odumegwu Ojukwu: Muhimman abubuwa 4 game da biloniyan farko na Najeriya

  • Duk da kowa ya san manyan ‘yan kasuwa irinsu Aliko Dangote, Femi Otedola, Tony Elumelu da sauran biloniyoyi ne masu kudin Najeriya, amma akwai wanda ya riga su shan kwana
  • Shi ne biloniya na farko duk fadin Najeriya, kuma shi ne shugaban farko na bangaren musayar jari na Najeriya, sannan sunansa Sir Louis Philip Odumegwu Ojukwu
  • Ya mallaki dukiyoyi masu yawa a fadin Najeriya da kasashen ketare, kudin da ya mallaka a darajarsu ta yanzu sun kai dala biliyan 4 daidai da N1,645,960,000,000

Duk da a lissafin masu kudin Najeriya kowa ya san manyan ‘yan kasuwa kuma biloniyoyi kamar su Aliko Dangote, Femi Otedola, Tony Elumelu da sauransu, amma akwai wani wanda duk ya riga su shan kwana.

Shi ne shugaban musayar jarin Najeriya na farko kuma sunansa Sir Louis Philip Odumegwu Ojukwu. An haife shi a 1909 kuma dan asalin Nnewi ne.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Louis Odumegwu Ojukwu: Muhimman abubuwa 4 game da biloniyan farko na Najeriya
Louis Odumegwu Ojukwu: Muhimman abubuwa 4 game da biloniyan farko na Najeriya. Hoto daga Chimere Ukoha Iroha
Asali: Facebook

Ya yi kokarin tara dukiyoyi masu yawa ta hanyar kasuwanci a Najeriya har da kasashen ketare.

Legit.ng ta gano abubuwa 4 dangane da mutumin wanda ya kai shekaru 57 kafin ya mutu.

1. Kamar yadda Forbes Africa ta ruwaito, a darajar kudi a yanzu, Sir Louis Odumegwu Ojukwu ya tara dala biliyan 4 wanda ya kai darajar N1,645,960,000,000.

Ya samu kudade masu yawa har ta kai ga ya taimaka wa turawa lokacin yakin duniya na biyu da motoci masu yawa wanda har sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II ta nada shi a matsayin sadauki.

2. Shine shugaban farko wanda yayi musayar jarin Najeriya na farko, ya shugabanci The African Continental Bank, Wikipedia.

Sauran kamfanoni da ko dai shine shugaba ko kuma dan kwamitin zartarwa sun hada da Nigerian Coal Corporation, Costain West Africa Ltd, John Holt, Nigerian Marketing Board da sauransu.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

3. Mahaifinsa dan kasar Biafra ne, Shugaba Odumegwu Ojukwu. Sir Lous ya mutu ana saura shekara daya a yi yakin farar hula amma mutane da dama ba su san shine mahaifin wanda ya fara kirkirar Biafra ba, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu.

Dansa, Ojukwu , shi ne wanda ya fara assasa raba kasar Biafra wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

4. Baya ga kasancewarsa dan kasuwa, har ila yau dan siyasa ne. Wikipedia ta tabbatar da cewa shi dan jam’iyyar NCNC, jam’iyyar da ta wanzu tsakanin 1944 zuwa 1966. Ya ci zaben dan majalisar wakilai a lokacin.

Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan

A wani labari na daban, shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.

Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng