Bayan auren 'yarsa, Sarkin Bichi ya kaddamar da aikin inganta wutar lantarki a Bichi
- Sarkin Bichi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana a zagayen masarautar Bichi
- An bayyana manufar shirin da cewa, za a karfafa 'yan kasuwa da manoma a yankin na Bichi
- Sarkin ya nemi hadinkan mazauna yankin domin tabbatar da nasarar aikin da za fara nan kusa
Kano - Mai martaba sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai karfin megawatt 8 a Bichi don inganta wutar lantarki a karkara da tabbatar da dorewar ci gaba, Daily Trust ta ruwaito.
Kimanin gidaje 12,000 a yankuna 40 daban-daban a cikin kananan hukumomi tara da ke karkashin masarautarsa za su ci gajiyar shirin samar da wutar lantarkin ta hasken rana.
Kamfanin Sandstream Nigeria Limited ne ya fara wannan aikin tare da hadin gwiwar hukumar samar da wutar lantarki ta karkara (REA) na gwamnatin tarayya.

Asali: UGC
Manufar aikin a Bichi shine rufe gibin makamashi tare da samar da hanyoyin samar da makamashin hasken rana don inganta hanyoyin samar da wutar lantarki da kuma taimakawa wajen bunkasa Kasuwar Dawanau zuwa da karfafa manoma a yankin.
Da yake jawabi a bikin kaddamar da aiki, shugaban kamfanin Sandstream Nigeria Limited, Alhaji Ibrahim Abba Gana, ya ce kamfanin zai tabbatar da nasara da dorewar aikin don taimakawa manoma da ‘yan kasuwa a Kasuwar Dawanau.
A nasa jawabin, sarkin Bichi ya yaba wa kamfanin da wadanda suka yi hadin gwiwa don bullo da hanyar samar da lantarki ta hasken rana a Bichi.
Sarkin ya kuma ce an kafa kwamiti wanda ya kunshi masu unguwanni da hakimai don zabar kauyukan da za su ci gajiyar shirin.
Ya kuma bukaci wadanda ke Kasuwar Dawanau da su ba da hadin kai wajen tabbatar da nasara da dorewar shirin.
An yi bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
Surukin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, zai amshi sandar girma a yau Asabar, 21 ga watan Agusta.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan daura auren ‘yarsa, Zahra Bayero da dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa tuni aka fara bikin wanda ke gudana a Masarautar Bichi da ke Jihar Kano.
Zuwa yanzu daga cikin manyan baki da suka hallara a wajen akwai Sultan na Sokoto kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Har ila yau, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda yakasance ɗan uwan sarkin na Bichi ya hallara a wajen bikin bayan rashin halartar ɗaurin Zarah da kuma Yusuf a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta.
Hakazalika mai alfarma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai ya hallara a wajen taron.
Sauran sune Sarakunan Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamali, na Daura Umar Farouk Umar, Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Lafiya, da mataimakin gwamnan Zamfara, da sauran su, Daily Trust ta ruwaito.
An tsaurara matakan tsaro tun daga mashigar garin tare da jami'an tsaro daban -daban da ke kokarin tabbatar da doka da oda.
Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku
A wani labarin, Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito.
Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.
Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.
Asali: Legit.ng