Murna ya lullube mahaifiyar tagwaye 'yan kwalisa da suka zama likitoci a rana daya

Murna ya lullube mahaifiyar tagwaye 'yan kwalisa da suka zama likitoci a rana daya

  • Wasu samari biyu 'yan tagwaye sun cimma wata nasasar rayuwa lokacin da suka zama likitoci
  • Mahaifiyarsu ta bayyana cewa, sun kammala karatun likita a makaranta daya, kuma a rana daya
  • Ta kuma bayyana irin kalubalen da suke fuskanta a kafafen sada zumunta saboda kamanceceniyarsu

Wasu samari kyawawa guda biyu, Chidimma Muogbo da Chinemerem Muogbo, wadanda tagwaye 'yan uwan juna ne sun kammala karatu a makarantar likitanci a matsayin likitoci.

Mahaifiyarsu, Uju Sussan mai digirin digirgir kuma babbar malama a Jami'ar Jihar Anambra ta Najeriya, ita ta yada labarin a shafinta na LinkedIn.

Baya ga taya 'ya'yanta maza biyu murna, mahaifiyar cikin alfahari ta kuma bayyana yadda suka fuskanci kalubale tare da dandamali daban-daban na kafofin sada zumunta da kuma tsarin tantancewa saboda kamanceceniyarsu.

Hotunan samari takwaye 'yan kwalisa da suka kammala karatun likatanci rana daya
Tagwayen Likitoci | Hoto: LinkedIn, Uju Sussan, PhD
Asali: UGC

Ta ambaci daya daga cikin irin kalubalen kamar haka:

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

"A makon da ya gabata akan wannan manhaja, LinkedIn #linkedincommunity, sun yi rubutu game da kammala karatunsu kuma sun ambaceni akai amma LinkedIn ya cire daya daga cikin rubutun tare da tunanin mutum daya ne ya yi, har sai da suka rubutawa LinkedIn ya maido da shafukan nasu."

Martanin jama'a kan wadannan takwaye

Bayan da ta yi wannan rubutu, mutane da dama sun yi martani yayin da suka ga wannan labari mai daukar hankali.

Chinonyelum Ejimuda ta ce:

"Na yi tsammanin ni da 'yar tagwaye ta, Chibundom Ejimuda ne kadai muka samu matsalar katin ID na kasa."

Iain Stewart Brown-Hovelt ya ce:

"Tsarin ba zai iya yin tunanin banbanta su ba saboda masu kirkirar basu kula ba..... masu kirkira sai ku lura. Ina taya su murnar cimma wannan aikin da suka yi na zama likitoci amma ina fatan ba za su yi aiki a asibiti daya ba ko kuma a sami marasa lafiya da yawa da zasu shiga rudu.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Mariel NievesClassen ya bayyana cewa:

"Ke uwa ta gari ce da kika ilimantar da tagwayen ki. Hakanan, za ki yi alfahari da hakan."

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

A wani labarin daban, wata budurwa ta bar kasar ta Rasha ta dawo nan gida Najeriya saboda sha’awar wasan barkwanci na ban dariya da ake yi anan wanda tuni ya dauki hankalinta.

Juliana Belova ita ce budurwar da ta bada mamaki bisa nuna ra'ayin da ba a saba ji ba, kasancewar mutane da dama na son barin Najeriya zuwa turai, amma ita ta baro turai zuwa Najeriya mai cike da albarka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel