Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari

Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari

  • Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta musanta rade-radin dake yawo na cewa jami'an da ke kula da CCTV a NDA suna bacci yayin da aka kai hari
  • Kamar yadda mai magana da yawun rudunar, Sawyer ya sanar, ya ce sanannen abu ne idan aka ce jami'ansu kwararru ne masu aiki tukuru
  • Ya tabbatar da cewa har a halin yanzu hedkwatar tsaron bincike take kuma za ta bankado tare da ladabtar da masu laifi a lamarin

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa, ta ce jami'anta dake kula da CCTV idon su biyu yayin da miyagun 'yan bindiga suka kutsa makarantar horar da hafsoshin soja ta NDA da ke Kaduna.

A take suka kashe hafsoshin soja biyu yayin da suka yi garkuwa da daya sannan suka raunata daya bayan mummunan harin da suka kai a sa'o'in farko na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Harin yan bindiga kan makarantar sojoji abun kunya ne – Kungiyar ACF

Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari
Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, an tabbatar da cewa jami'an da ke kula da CCTV na NDA suna sharar baccinsu ne yayin da wannan mummunan harin ya auku.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an damke dukkan hafsoshin sojojin da ke dakin kuma ana ladabtar da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kuma a wata takarda da hedkwatar tsaro ta fitar a ranar Laraba, ta ce wannan zargin bashi da tushe, TheCable ta wallafa.

Akwai matukar amfani a sanar da cewa AFN tana daukar jami'ai ne masu matukar kwarewa wadanda ke da dagewa wurin sauke nauyin baiwa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya," takardar da Benjamin Sawyerr, mai magana da yawun DHQ ya fitar.
Bari in yi amfani da wannan damar wurin tabbatar da cewa, hukumomin NDA suna aiki da umarnin shugaban ma'aikatan tsaro kuma an kafa kwamitin bincike wanda zai bankado tushen matsalar tsaron da aka samu kuma za a tabbatar da an ladabtar da masu laifi tare da hana aukuwar makamancin hakan nan gaba.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Muna tabbatar muku da cewa za mu cigaba da sanar da jama'a duk wani abinda ke faruwa kuma ana cigaba da neman hafsan sojan da aka sace.
Dakarun soji na kasar Najeriya za su cigaba da aiwatar da ayyukansu domin tabbatar da cewa an bankado miyagu tare da ladabtar da su.

IGP ya bullo da sabbin hanyoyin maganin 'yan bindiga a jihar Zamfara

A wani labari na daban, Sifeta janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Baba ya kawo sabuwar hanyar kawo karshen rashin tsaron da jihar Zamfara take fuskanta.

AIG na Zone 10 na jihar Sokoto, Ali Janga ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara a kan wannan rashin tsaron da jihar ta ke fuskanta, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da ‘yan sanda da yayi a Gusau, AIG ya ce IGP ya sauya hanyar kawo karshen rashin tsaron da jihar Zamfara da sauran jihohi suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel