Gwamnan Enugu ya sake gina Masallatai biyu da aka kona lokacin zanga-zangar EndSARS
- Bayan kimanin shekaru guda da kona Masallatai biyu, an sake ginasu
- Wasu lalatattun matasa sun bankawa Masallatan wuta lokacin zanga-zangar EndSARS
- Al'ummar Musulmai a yankin sun jinjinawa gwamnan jihar da wannan abu
Nsukka, Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, a ranar Juma'a ya kammala ginin Masallatai biyu dake garin Nsukka da aka lalata lokacin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.
Gwamnan ya mika Masallatai ga al'ummar Musulman Nsukka.
Bayan rikicin da ya auku lokacin, gwamnan ya umurci shugaban karamar hukumar Nsukka, Cosmas Ugwueze, ya hada kai da al'ummar Musulman garin don sake ginin Masallatan.
A taron bude Masallatan da aka yi, gwamnan wanda ya samu wakilcin Mr Ugwueze ya godewa Musulmai da Kiristocin yankin bisa zaman lafiyan da sukeyi, kuma ya tabbatar musu da cewa zai cigaba da kare lafiyar kowa a jihar.
A sakon godiyar shugaban al'ummar Musulmin Nsukka, Farfesa Momoh Mumuni, ya aikewa gwamnan, ya gode masa bisa sake gina Masallatan.
Farfesa Momoh yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan ya nuna "halinsa na tausayi, jajircewa, hakuri, hada kan jama'a da kuma ikhlasi wanda tuni mun sani cewa ba ka gaba da kowa dake zaune da kai."
Babban Limamin Masallacin Nsukka, Yakubu Omeh, ya godewa Allah babu wanda ya rasa rayuwarsa lokacin zanga-zangar kuma ya jinjinawa gwamna Uguwanyi bisa kokarinsa.
Wasu matasa sun kona Masallatai biyu da shaguna 14 a Jos
A jihar Plateau kuwa, Wasu fusatattun matasa sun kona Masallatai biyu tare da kona shaguna 14 a kasuwar kayan gine-gine dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.
A cewar Daily Nigerian, shugaban masu sayar da kayan miya a kasuwannin jihar, Dalyop Pwasa, ya tabbatar da hakan.
Yace:
"Da gaske ne cewa wasu mutane sun shiga kasuwarmu ranar Laraba, sun fasa wasu shaguna, sun sace kayayyaki kuma sun kona shaguna 14."
"Sun lalata Masallatai biyu dake cikin kasuwar."
Hakazalika Sakataren kungiyar yan kasuwa, Fodio Umar, ya yi karin haske kan abinda ya faru inda yace an kona Masallatan biyu kurmus duk da dokar hana fita da gwamnan ya sa.
Asali: Legit.ng