Da dumi: Wasu matasa sun kona Masallatai biyu da shaguna 14 a Jos
- Rikicin jihar Plateau ya ki ci, ya ki cinyewa har yanzu
- Bayan kisan kimanin mutane 35 a garin Yelwa, wasu sun kai hari kasuwa
- Sun kona Masallatai biyu tare da shagunan mutane duk da dokar ta baci da aka sanya
Jos - Wasu fusatattun matasa sun kona Masallatai biyu tare da kona shaguna 14 a kasuwar kayan gine-gine dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.
A cewar Daily Nigerian, shugaban masu sayar da kayan miya a kasuwannin jihar, Dalyop Pwasa, ya tabbatar da hakan.
Yace:
"Da gaske ne cewa wasu mutane sun shiga kasuwarmu ranar Laraba, sun fasa wasu shaguna, sun sace kayayyaki kuma sun kona shaguna 14."
"Sun lalata Masallatai biyu dake cikin kasuwar."
Hakazalika Sakataren kungiyar yan kasuwa, Fodio Umar, ya yi karin haske kan abinda ya faru inda yace an kona Masallatan biyu kurmus duk da dokar hana fita da gwamnan ya sa.
Yace:
"Lallai wasu batagari sun rusa Masallatai biyu dake cikin kasuwarmu."
"Sun fara rusawa ne ranar Laraba kuma suka karasa ranar Alhamis kuma sun rusa su gaba daya har kasa."
Malam Fodio ya kara da cewa sun fasa wasu shaguna kuma sun bankawa wasu wuta.
A cewarsa, an kai kara ofishin yan sanda dake Sabon Barki, kuma an bukaci Limaman Masallatan biyu su je ofishin.
Ya ce har yanzu basu samu daman zuwa duba irin barnar da akayi musu ba saboda dokar hana fita da gwamnatin ta sa.
Yace:
"Dokar ta baci ta hanamu zuwa ganin irin barnar da akayi. Shugabanmu kadai ke wajen.
"Mr Dalyop Pwasa yana iyakan kokarinsa. Shi ya nemo motoci suka kwashe da mayanmu daga cikin kasuwar. Shi ya kira yan kwana-kwana suka kashe wutar."
Asali: Legit.ng