'Yan ta'adda 27 sun sheka lahira bayan rikici ya barke tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP

'Yan ta'adda 27 sun sheka lahira bayan rikici ya barke tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP

  • Wani rikici da ya barke tsakanin mayakan ISWAP da na Boko Haram ya janyo rashe-rashen rayuka tsakanin 'yan kungiyoyin guda biyu
  • An samu rahotanni a kan yadda fusatattun mayakan ISWAP suka kai wa dimbin 'yan Boko Haram da suka yi nufin zubar da makamansu a kauyen Dumbawa
  • Sun kai wa 'yan Boko Haram farmaki ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Augustan a daidai iyakar Nijar lokacin da suke hanyar zuwa wurin MNJTF don tuba

Borno - 'Yan Boko Haram da mayakan ISWAP da dama sun rasa rayukansu bayan wani mummunan karon batta da ya auku tsakanin kungiyoyin guda biyu da ke arewacin Abadam a jihar Borno.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai a kan yadda 'yan Boko Haram da dama suka rasa rayukansu bayan fusatattun mayakan ISWAP da ke wuraren Gusuriya a kauyen Dumbawa sun kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Mutum 16 Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Ragargaji Mayakan Boko Haram 50 a Nijar

'Yan ta'adda 27 sun sheka lahira bayan rikici ya barke tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP
'Yan ta'adda 27 sun sheka lahira bayan rikici ya barke tsakanin 'yan Boko Haram da ISWAP. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

'Yan Boko Haram suna hanyar zuwa mika da makamansu ga MNJTF a daidai iyakar Nijar ranar Lahadi, 22 ga watan Augustan 2021 aka kai musu farmaki.

Daya daga cikin jami'an tsaro na sirri ya bayyana yadda shugabancin mayakan ISWAP ya lalace tun bayan fara mubaya'ar 'yan Boko Haram, hakan yasa suka yanke hukuncin kisa ga duk wanda ya sake tserewa daga tafkin Chadi.

Wani Abba Kaka ne ya shirya harin, wanda gwamna ne shi na Tumbumma kuma kwamandan Marte, Kukawa da Magumeri, lamarin da ya janyo karon batta tsakaninsu na sa'o'i da dama kuma mayaka fiye da 25 ne suka rasa rayukansu sannan sauran wadanda suka tsere tare da iyalansu suka samu miyagun raunuka sakamakon harbe-harben bindigogi.

Wata majiyar ta sanar da PRNigeria ta ce rikici tsakanin kungiyoyin guda biyu zai cigaba da barkewa sakamakon kin nada 'yan Boko Haram a manyan mukamai.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan Boko Haram kan mika wuya, sun kashe juna 27

An rage wa manyan kwamandojin Boko Haram masu matsayin Amir da Khalid lokacin mulkin Shekau mukami inda aka mayar da su mayaka kawai sannan aka nada mayakan ISWAP a manyan mukamai.
Wasu daga cikin tsofaffin kwamandojin Boko Haram sun fara tunanin hada kai da bangaren mayakan Boko Haram na Bakura da Krimima don fara yakar 'yan ISWAP da ke wuraren Lelewa, Duwa, Wallal da kauyen Hauwa da ke jamhuriyar Nijar,"kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Ku binciki hanyar samun kwastomomin ku, EFCC ga bankuna

A wani labari na daban, shugaban EFCC ya umarci bankuna a kan bincike hanyoyin samun kudaden abokan harkokin su.

Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya furta hakan a ranar Talata lokacin da ACAEBIN ya kai masa ziyara har Abuja.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, Bawa ya ce akwai abokan huldar banki da makudan kudade za su shiga asusunsu cikin watanni biyu da bude asusun bankin.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: