Da Ɗuminsa: Jirgi Mai Saukan Ungulu Ya Buɗe Wa Fasinjojin Jirgin Ruwa Wuta a Rivers, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

Da Ɗuminsa: Jirgi Mai Saukan Ungulu Ya Buɗe Wa Fasinjojin Jirgin Ruwa Wuta a Rivers, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

  • Wani jirgi mai saukan ungulu da ba a tabbatar na wanene ba ya bude wa jirgin ruwa wuta a Bonny
  • Wani ganau ya bayyana cewa jirgin ruwan ya tashi daga Bonny ne yana kan hanyarsa na zuwa Fatakwal
  • Shaidan ganin na ido ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen jirgin sun mutu yayin da saura an garzaya da su asibiti

Jihar Rivers - Wani jirgi mai saukan ungulu da a yanzu ba a gano mallakar waye ba ya harbi wani jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji daga Fatakwal zuwa Bonny a jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Ana fargabar wasu sun mutu, yayin da wasu daga cikin wadanda ke cikin jirgin an kwashe su zuwa asibiti.

Da Ɗuminsa: Jirgi Mai Saukan Ungulu Ya Buɗe Wa Fasinjojin Jirgin Ruwa Wuta Rivers, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu
Jirgi Mai Saukan Ungulu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Abin da wani ganau ya ce game da afkuwar lamarin?

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu

Wani shaidan gani da ido a bakin ruwa na Bonny-Nembe inda abin ya faru ya ce jirgin ya taso ne daga Fatakwal, ya kuma shaidawa manema labarai akwai wadanda suka mutu, a cewar SaharaReporters.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ke bayyana fargabarsa kan faruwar lamarin, ya ce jirgin ruwan na dauke da fasinjoji da kayan abinci.

Ya yi ikirarin cewa:

"Jirgin ruwan bai dade da barin nan Bonny ba, a tsibirin, wata helicofta ko jirgi mai saukan ungulu, kawai ta zo ta baya, ta sako kasa-kasa ta fara budewa jirgin ruwan na katako wuta.
"Daga bayannan da muka samu daga direban jirgin ruwan, akwai fasinjoji a jirgin, Kazalika akawai kayan abinci kamar garin rogo, shinkafa da wasu kayan abincin.
"Kowa ya san cewa wannan ne hanyar da ake jigilar abinci zuwa Bonny. Wasu mutane sun mutu a cikin jirgin ruwan."

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Ba a samu ji ta bakin hukumomin tsaro ba

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni ya ce bai riga ya samu rahoton ba.

Kakakin sojojin Nigeria, 6 Division, Charles Ekeocha, shi kuma bai daga wayarsa ba, haka ma takwararsa na rundunar sojojin sama a Fatawal, a lokacin hada wannan rahoton.

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel