Da duminsa: Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu
- Abokan siyasa da suka zama abokan hamayya sun sake haduwa da juna
- Kwankwaso ya kasance maigidan Ganduje na tsawon shekaru amma abubuwa suka tabarbare tsakaninsu
- Jiga-jigan siyasan biyu zasu hau jirgi daya zuwa Kano
Abuja - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da magabacinsa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sun hadu bayan shekara da shekaru.
Tsaffin abokan siyasan sun hadu ne a sashen VIP na tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja, DailyNigerian ta ruwaito.
Sun zauna dakin ne yayinda suke shirin hawa jirgi don zuwa jihar Kano.
Jagororin biyu sun dade suna wasan buya tun lokacin da suka samu sabani bayan zaben 2015.
Wannan ba shine karo na farko da zasu hadu a filin jirgi na
A ranar 6 ga watan Satumba, 2018, mun kawo muku cewa tawagar Kwankwaso ta gamu da ta Ganduje a filin jirgin sama.
Kamar dai yadda muka kawo muku lokacin, tawagar fitattun 'yan siyasar dai sun hadu ne a filin jirgin jihar Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda akayi sa'a dukkan su sun je a ranar Laraba
Manyan dalilan da su ka harzuka wutar rikicin Kwankwaso da Ganduje
1. Bashin Biliyoyin kudi
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa tsohon Maigidan sa ya bar wa Jihar Kano bashin biliyoyi na kudin ‘yan kwangila. Daga ciki akwai kudin ‘yan fansho da aka dauka aka gina gidajen da su ka zama ala-ka-kai. Sai dai Gwamnatin sa tayi da gaske za ta iya biyan wannan kudi.
2. Kudin makarantar ‘Dalibai
Akwai nauyin kudin makarantar ‘daliban da aka tura kasar waje da ya kai Naira Biliyan 4 da ke wuyan Gwamna Ganduje. Bayan wannan ma akwai wasu makarantu da Kwankwaso ya bude a Kano wadanda dama can ya san ba za su kai ko ina ba sai dai ya hada Magajin sa da aiki.
3. Sukar Gwamnati da katsalandan
Gwamna Ganduje ya tafi da wasu manyan na hannun-daman Kwankwaso ko da dai bai zabi da dama daga Kwamishinonin sa ba sai dai kuma wasu ‘Yan Kwankwasiyya da manyan APC a da sun rika sukar Gwamnan har a lokacin da ake zaman makokin Mahaifiyar sa wanda bai ji dadin hakan ba.
Shi dai Gwamna Ganduje yana ganin babu wanda zai nuna masa yadda zai tafiyar da Gwamnatin sa kuma yace tsohon Gwamnan ne ya hana su sasanta rikicin na su.
Asali: Legit.ng