Ronaldo ya bukaci ya bar Juventus, ya na tangaririn neman wanda zai iya biyan albashinsa

Ronaldo ya bukaci ya bar Juventus, ya na tangaririn neman wanda zai iya biyan albashinsa

  • Cristiano Ronaldo ya fada wa Juventus cewa yana bukatar barin kulob din
  • Dillalin ‘dan kwallon, Jorge Mendes ya shiga nema masa inda zai koma wasa
  • Akwai yiwuwar Ronaldo ya tafi kungiyar tsofaffin abokan gabansa a Ingila

Babban ‘dan wasan Duniya, Cristiano Ronaldo ya shaida wa kungiyar Juventus cewa yana bukatar tashi daga kulob din tun kafin kwantiraginsa ya kare.

Cristiano Ronaldo: Zan bar Juventus

Shahararren ‘dan jaridar nan, Fabrizio Romano, ya bayyana haka a shafinsa a ranar Juma'a, 27 ga watan Agusta, 2021, yace ‘dan wasan yana neman kulob.

Dillalin ‘dan wasan na Portugal, Jorge Mendes, yana tattauna wa kai tsaye da kungiyar Manchester City domin ganin yiwuwar ya koma kwallo a can.

Sai dai babu tabbacin Cristiano Ronaldo zai cigaba da karbar albashin da yake karba a Juventus idan ya tashi. Ana biyan ‘dan wasan fam €31m a shekara.

An iya cin ma yarjejeniya?

Sky Sports News tace an yi wa Manchester City tayin Ronaldo a jiya, amma ba a iya cin ma yarjejeniya tsakanin dillalin ‘dan wasan da Juventus ba.

Juventus tana neman akalla fam £25m a kan ‘dan wasan mai shekara 36 wanda ta saya a 2018.

Ronaldo
Cristiano Ronaldo Hoto: www.news24.com/sport
Asali: UGC

Ita kuma Manchester City tana so ta dauki ‘dan kwallon ne kyauta, ta ba shi kwantiragin shekara biyu da zai rika karbar fam £12.8m a kowace shekara.

Ganin ya sayo Jack Grealish a kan miliyan £100m a kakar bana, Pep Guardiola bai da niyyar sake kashe kudi duk ana rade-radin yana harin Harry Kane.

Cristiano Ronaldo zai so ya dawo Ingila?

Ko da Koci Guardiola bai sha’awar tsohon tauraron na Real Madrid, kungiyar City za ta iyo dauko ‘dan kwallon idan ta ga za ta samu riba a wannan ciniki.

Irinsu Wayne Rooney suna ganin cewa ‘dan wasan gaban ba zai buga wa Manchester City ba ganin kungiyar Manchester United ce ta fito da shi a Duniya.

Rade-radin PSG

A jiya ne aka ji cewa Real Madrid ta mika kusan Naira Biliyan 80 domin ta dauke Kylian Mbappe daga PSG ganin 'dan wasan ya ki sabunta kwantiraginsa.

Ana tunanin idan Mbappe ya koma Real Madrid, kungyar Paris Saint-Germain za ta iya dauko Cristiano Ronaldo, ya hadu da taurari irinsu Lionel Messi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel