Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

  • Yayin da 'yan Najeriya ke sha'awar barin gida Najeriya zuwa turai, wata baturiya ta dawo Najeriya
  • A cewarta, Najeriya ta ba ta sha'awa, wannan yasa ta yanke shawarar dawowa Najeriya da zama kawai
  • Ta samu mabiya, ta kuma koyi abubuwan 'yan Najeriya da dama ciki har da shahararren turancin Pidgin

Wata budurwa ta bar kasar ta Rasha ta dawo nan gida Najeriya saboda sha’awar wasan barkwanci na ban dariya da ake yi anan wanda tuni ya dauki hankalinta.

Juliana Belova ita ce budurwar da ta bada mamaki bisa nuna ra'ayin da ba a saba ji ba, kasancewar mutane da dama na son barin Najeriya zuwa turai, amma ita ta baro turai zuwa Najeriya mai cike da albarka.

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta
Oyibo Marlian | Hoto: @oyibomarlian
Asali: UGC

Meye dalilin da yasa ta yanke wannan shawara mai kyau?

Kara karanta wannan

Budurwa ta kashe N904,000 don likitoci su kara mata girman labba da fuska

A wata hira da aka yi da ita a shirin TVC mai suna Wake Up Nigeria, budurwar da aka fi sani da 'Oyibo Marlian' ta bayyana cewa kawai ta fada matukar kaunar wasan barkwanci na ban dariya na Najeriya ne.

'Oyibo Marlian' ta ce yayin da take a kasar Rasha, ta yi sha'awar yadda ake sarrafa salon wasan kwaikwayo na ban dariya wanda ya sha bamban da abin da ake samu a kasar haihuwar ta; Rasha ko Amurka.

Juliana ta ce ta kan kalli wasan barkwanci a tsawon lokaci a kan kafar sada zumunta na kawayenta 'yan Najeriya don haka ta yanke shawarar ta dawo gida Najeriya da zama.

Da jakarta da kudi N41,000 kacal ta shigo Najeriya

Juliana, a cewar rahotannin Vocal Media, ta bar Rasha daga ita sai jakar kayanta da kudi $100 (N41,000) kasancewar ta rasa aikinta a lokacin barkewar cutar Korona.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Kudin da ta zo Najeriya da shi an ce wani dan a-mutun ta ne ya ba ta a kafar sada zumunta ta Instagram.

Abin da take yi a Najeriya

Gaskiyata kalamanta, tun zuwanta Najeriya, budurwar ta tsunduma cikin harkar wasan barkwanci, tana burge mabiyanta na kafafen sada zumunta na zamani lokaci zuwa lokaci inda take daura bidiyon rawa na wasan barkwanci.

'Oyibo Marlian', kamar yadda ake kiranta, ta iya yaren Pidgin kuma an ce tana matukar kaunar wakokin mawakiyar Najeriya Naira Marley kuma ta nuna hakan a cikin raye-rayen da take yadawa.

Tana da mabiya sama da dubu 100 a shafinta na Instagram, Juliana ta yi wasanni tare da shahararre Don Jazzy da sauran masu wasan barkwanci na A-list ciki har da Lord Lamba.

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

A wani labarin, Legit ta tattaro muku labari mai kamar almara, yayin da bincike ya bankado cewa, akwai wani gari a kasar Italiya, inda mutum zai iya mallakar gida da karamin kudin da bai haura £1 wanda yake kwatankwacin N483.28 na Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta sammaci yar wasar Kannywood, Ummah Shehu

Yanzu haka a garin mai suna Maenza ana siyar da tsoffin gidaje kuma an ba da rahoton cewa karin iyalai na tururuwan fitowa don sayar da tsoffin gidajensu.

Mutane da dama za su ga wannan batu ba komai bane illa zamba, duk da haka, an nakalto magajin garin Claudio Sperduti a kafafen yada labarai daban-daban da ke tabbatar da yarjejeniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel