Da Ɗumi-Ɗumi: Ku mayar da hankali kan tsaro maimakon suka ta, Ortom ya yi wa Fadar Shugaban Kasa martani

Da Ɗumi-Ɗumi: Ku mayar da hankali kan tsaro maimakon suka ta, Ortom ya yi wa Fadar Shugaban Kasa martani

  • Gwamna Samuel Ortom ya ragargaji fadar shugaban kasa bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya janyo kisar kare dangi
  • Gwamnan na Jihar Benue ya bukaci fadar shugaban kasar ta kyalle shi ta mayar da hankali kan tsaro da tattalin arziki
  • Ortom ya zargi fadar shugaban kasa da kitsa tugu domin janyo rikici a jiharsa da zai sa a saka dokar ta baci daga gwamnatin tarayya

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bukaci fadar shugaban kasa ta mayar da hankali wurin magance matsalar rashin tsaro da kashe yan Nigeria da ake yi maimakon sukarsa, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labaransa Terver Akase ya fitar a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton

Da Ɗumi-Ɗumi: Ku mayar da hankali kan tsaro maimakon suka ta, Ortom ya yi wa Fadar Shugaban Kasa martani
Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Benue Samuel Ortom. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An dade ana dauki ba dadi tsakanin Ortom da fadar shugaban kasa

Fadar shugban kasar ta kasance tana musayar maganganu da Ortom a 'yan kwanakin baya-bayan nan.

Gwamnan na Benue, cikin wata hira da aka yi da shi a cikin yan kwanakin nan ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da yunkurin 'mayar da kasar ta Fulani' yayin da ya ke martani kan amincewa da shawarwarin kwamitin da aka kafa kan fulayen kiwo 368 a jihohi 25 na kasar.

Fadar shugaban kasar ta zargi Ortom da amfani da kalamai da ka iya janyo rikici da kisar kare dangi tamkar na kasar Rwanda.

A martaninsa Ortom ya ce abin da ya fada ra'ayin yan Nigeria ne da dama kan yadda fadar shugaban kasar ta gaza daukan matakin magance makiyaya fulani masu kisa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Ortom ya jadada cewa bai janye abin da ya fada ba kuma ba zai yi shiru ba.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Abin da gwamnan ya fada ra'ayin 'yan Nigeria ne da dama musamman a bangaren da fadar shugaban kasa ta gaza daukan mataki kan makiyaya fulani masu kisa da sauran yan ta'adda."
"A maimakon tattaunawa da gwamnan kan abin da ya fada, Shehu ya rika kame-kame yana wasu maganganu na kokarin bata sunan gwamnan.
"Muna bukatar neman afuwa daga fadar shugaban kasa bisa zargin Gwamna Ortom da furta kalaman da ka iya janyo kisar kare dangi. Fadar shugaban kasar bata taba boye kiyayyar da ta ke yi wa gwamnan ba, kalaman nan na baya-baya sun tabbatar da hakan.
"Mun san tugun da fadar shugaban kasa ke shiryawa na tada rikici a Benue don samun ikon saka dokar ta baci. Za zarar sun gaza cimma burinsu sai su fara sharri.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bama-bamai biyu sun tashi a kusa da filin jirgi a kasar Afghanistan

"Sun zargi gwamnan da korar Fulani daga Benue; ikirarin da ke nuna ba su karanta dokar hana kiwo a fili ba da kafa wuraren kiwo na zamani. Ba za su iya cewa gwamnan baya son Fulani ba duba da wasu yan fadarsa fulani ne.
"Muna shawartar fadar shugaban kasa ta mayar da hankali ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Nigeria, ta kuma inganta tattalin arziki da dakatar da rashawa da ake yi a gwamnati."

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164