Yanzu-yanzu: Bama-bamai biyu sun tashi a kusa da filin jirgi a kasar Afghanistan

Yanzu-yanzu: Bama-bamai biyu sun tashi a kusa da filin jirgi a kasar Afghanistan

  • Akalla mutum 11 sun mutu sakamakon harin Bam a birnin Kabul
  • Wannan ya biyo bayan labarin leken asiri da Amurka na cewa ana shirin kai hari
  • Gwamnatin Taliban bata bayyana adadin wadanda suka jigata ba har yanzu

Kabul - Babban Bam ya tashi a wajen tashar jirgin saman Hamid Karzai dake kasar Afghanistan yayinda jirage ke cigaba da kwasan yan kasar dake son komawa Amurka, Hukumar Sojin Amurka ta sanar da hakan.

Kakakin hedkwatar Sojin Amurka Pentagon, John Kirby, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki, rahoton Aljazeera.

Yace:

"Muna masu tabbatar da cewa Bam ya tashi a wajen tashar jirgin Kabul. Mun sake samun labarin cewa wani Bam ya sake tashi a kofar Abbey kuma akwai ya Amurka cikin wadanda suka jikkata."

Gwamnatin Amurka a farkon makon nan ta samu labarin leken asiri cewa wasu yan kunar bakin wake na shirin kai hari filin jirgin saman.

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Wani jami'in Taliban yace mutane 11 ne aka tabbatar sun mutu kawo yanzu, cewar AlJazeera.

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar da haramta kida a Afghanistan saboda "Ba Musulunci ba ne".

Wannan batu na kunshe ne a cikin wata hira da jaridar New York Times da kakakin kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta.

Sai dai ya lura cewa Taliban na fatan shawo kan mutane su yi biyayya ga sabuwar dokar, maimakon tilasta musu.

Haramcin zai zama kamar dawo da daya daga cikin tsauraran dokoki na mulkin kungiyar Taliban ta 1990, lokacin da aka hana yawancin nau'ikan kade-kade, ban da wakokin addini.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng