Da Dumi-Dumi: NBC Ta Tuhumi Channels TV Kan Tattaunawa da Gwamna Ortom
- Hukumar NBC ta kasa ta tuhumi kafar watsa labarai ta channels tv bisa tattaunawa da Gwamna Ortom
- NBC ta aike da takarda ga kafar tare da bata wa'adin kwana ɗaya tayi bayani dalla-dalla kan watsa kalaman gwamnan
- Ortom ya shahara wajen sukar shugaba Buhari da gwamnatinsa musamman kan maganar kiwon fili
Abuja - Hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasa (NBC), ta tuhumi Channels tv kan maganganun da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yi a shirinta na Sunrise daily ranar Talata.
Hukumar NBC ta bayyana hakane a wata takarda da ta aike wa kafar watsa labaran, kamar yadda punch ta ruwaito.
Takardar tana ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Agusta, kuma shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilelah, ya saka hannu.
NBC tace:
"Shirin wanda ya samu bakuncin zababben gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya kunshi kalaman zuga da rarrabuwar kai, wanda masu gabatar da shirin basu tsaftace su yadda ya kamata ba."
"Kuma yin hakan ya saɓa wa sashi na 1.10.4, 3.1.1, 3.3.1(b), 3.3.1(e), 3.11.1(a), da kuma 3.12.2 na dokokin watsa labarai a Najeriya."
"Saboda haka muna bukatar channels tv ta yi karin bayani kan dalilin da zai sa ba za'a ɗauki mataki a kanta ba bisa hawan kawara da tayi wa dokokin watsa labarai na kasa."
"Muna sauraron amsoshin ku cikin awanni 24 bayan wanan takardar ta isa gare ku."
Wane maganganu Ortom ya yi?
Ortom, wanda ya bayyana a cikin shirin, yace:
"Shugaban ƙasa na sakani tunanin ko abinda ake faɗa kansa cewa yana da wata ɓoyayyar manufa ga ƙasar nan gaskiya ne."
"Saboda komai ya fito fili yana son maida ƙasar nan ta fulani kuma ba shine bafullatani na farko da ya shugabanci kasar nan ba."
Shagari ɗan fulani ne, haka ma Yar'adua kuma tarihi ba zai manta da gudummuwarsu ba. Amma Buhari shine shugaban ƙasa mafi lalacewa idan ana magana kan tsaro da cika alƙawari."
Kokarin Buhari na samar da wurin kiwo da fulani
Gwamnan ya kuma caccaki shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan matakin da ya ɗauka game da kiwon fili, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa shugaba Buhari ya amince da shawarwarin kwamiti na sake duba filayen kiyo 368 dake jihohi 25 na kasar nan domin zamanantar da kiwo.
Da yake martani, Gwamna Samuel Ortom yace:
"Idan shugaban ƙasa yana bin doka, dokar amfani da filaye ta baiwa gwamnoni ikon zartar da abinda za'a yi da filaye a madadin al'ummar da suke jagoranta."
"Abin yana bani mamaki shugaban ƙasa ya yi irin haka kamar ba shi da Antoni janar da lauyoyi a tare da shi, waɗanda ya dace su ba shi shawara."
"Ina tunanin ba'a rawaito dai-dai ba ko kuma shugaban kasa yayi haka ne bisa kuskure. Don haka ya fito ya nemi gafarar yan Najeriya."
A wani labarin kuma Gwamnoni Sun Aike da Muhimmin Sako Ga Gwamna Zulum Kan Kyakkyawan Jagorancinsa
Kungiyar gwamnonin APC ta aike da sakon taya murnar ranar haihuwa ga gwamna Babagana Umaru Zulum.
Gwamnonin sun bayyana cewa Zulum na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da matsalar tsaro a faɗin Najeriya.
Asali: Legit.ng