Budurwa ta kashe N904,000 don likitoci su kara mata girman labba da fuska

Budurwa ta kashe N904,000 don likitoci su kara mata girman labba da fuska

  • Anastasiia Pokreshchuk ta zama daya daga cikin masu kumatu mafi girma a duniya
  • Yar-shekara-32 din ta fito ne daga birnin Kyiv, kasar Ukraine
  • Ta kashe £1,600 (N904,397.01) don ayi mata wannan allura

Wata budurwa yar kasar Ukraine mai suna, Anastasiia Pokreshchuk, ta shiga jerin mata masu manyan labba a duniya bayan Likitoci sun yi mata aikin Tiyata.

Daily Mail ta ruwaito cewa Anastasiia ta kashe kudi £1,600 (N904,397.01) wajen yi mata allura don kara girman labba.

Ta bayyana cewa ko kadan ba ta nadaman wannan abu da tayi kuma wannan yin kanta ne ba kwaikwayon wata tayi ba.

Budurwa ta kashe N904,000 don likitoci su kara mata girman labba da fuska
Budurwa ta kashe N904,000 don likitoci su kara mata girman labba da fuska Hoto: (@_just_queen)
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

A hirar da tayi kan shirin This Morning Today tare da Dr Steve Harris, budurwar ta jaddada cewa fuskarta yanzu na kara mata karfin gwiwa.

Tace:

"Abinda nayi ba komai bane kuma yana da kyau gareni, ban zan taba sauraran Likitoci ba."
"Ina farin ciki sosai. Da na kalli tsaffin hotuna na sai naga ina da muni."

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

Wata budurwa ta bar kasar ta Rasha ta dawo nan gida Najeriya saboda sha’awar wasan barkwanci na ban dariya da ake yi anan wanda tuni ya dauki hankalinta.

Juliana Belova ita ce budurwar ta ba da mamaki bisa nuna ra'ayin da ba a saba ji ba, kasancewar mutane da dama na son barin Najeriya zuwa turai, amma ita ta baro turai zuwa Najeriya mai cike da albarka.

A wata hira da aka yi da ita a shirin TVC mai suna Wake Up Nigeria, budurwar da aka fi sani da 'Oyibo Marlian' ta bayyana cewa kawai ta fada matukar kaunar wasan barkwanci na ban dariya na Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel