Da dumi: Majalisar dattawan PDP da NWC sun shiga ganawar gaggawa kan rikicin jam'iyyar

Da dumi: Majalisar dattawan PDP da NWC sun shiga ganawar gaggawa kan rikicin jam'iyyar

  • Biyo bayan dakatar da Secondus, dattawan PDP na shirin dinke barakar jam'iyyar
  • An shiga zaman tattaunawa na gaggawa yanzu haka a hedkwatar PDP
  • Daga cikin mahallara akwai Atiku, David Mark, Walid Jibrin dss

Abuja - Kwamitin gudanarwa da majalisar dattawar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP sun shiga ganawar gaggawa a hedkwatar jam'iyyar. Wadata Plaza, Abuja.

Kwamitin ta samu halartan daukacin mambobinta karkashin mataimakin shugaban jam'iyyar (Yankin kudu), Yemi Akinwumi.

Sauran dake hallare a zaman sune mataimakin shugaban jam'iyyar (Arewa), Sanata Suleiman Nazif; Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbodiyan, da shugaban matasan jam'iyyar, Sunday Ude-Okoye, dss.

An fara wannan ganawar ne misalin karfe 12 na rana.

Da dumi: Majalisar dattawan PDP da NWC sun shiga ganawar gaggawa kan rikicin jam'iyyar
Da dumi: Majalisar dattawan PDP da NWC sun shiga ganawar gaggawa kan rikicin jam'iyyar Hoto: OfficialPDP
Asali: Twitter

An fara zaman majalisar BOT

A bangaren majalisar dattawar jam'iyyar kuwa, za'a fara zaman yanzu.

Wadanda suka dira hedkwatar PDP don ganawar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; mataimakin shugaban majalisa, David Mark; tsohon sakataren gwamnati, Anyim Pius Anyim.

Sauran sune shugaban majalisar dattawar PDP, Walid Jibrin; tsohon shugaban Soji, Janar Ishaya Bamaiyi; tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, dss.

PDP ta rabu gida 2, sabbin shugabannin jam'iyya 2 sun bayyana

Kawunan magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP sun rabu gida biyu tun bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus da babbar kotun Jihar Fatakwal tayi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Litinin, kotu ta dakatar da Secondus daga zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Sakamakon hakan ne mataimakin shugaban jam’iyyar na bangaren kudu, Elder Yemi Akinwonmi, ya baje kafada a kan shi ya fi cancanta ya shugabanci jam’iyya.

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

Wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel