Da duminsa: PDP ta rabu gida 2, sabbin shugabannin jam'iyya 2 sun bayyana

Da duminsa: PDP ta rabu gida 2, sabbin shugabannin jam'iyya 2 sun bayyana

  • Kawuna sun rabu gida biyu tun bayan babbar kotun Fatakwal ta dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus
  • Tun bayan nan, mataimakan shugaban jam’iyyar na Kudu da arewa suke ta sa-in-sa, kowa yana fadin shi ya cancanci darewa kujerar shugabancin
  • Sai dai, magoya bayan mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa, Sanata Suleiman Nazif, har sun sanya ranar 27 ga watan Augusta a matsayin ranar taron NEC na jam’iyyar

Fatakwal - Kawunan magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP sun rabu gida biyu tun bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus da babbar kotun Jihar Fatakwal tayi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Litinin, kotu ta dakatar da Secondus daga zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Da duminsa: PDP ta rabu gida 2, sabbin shugabannin jam'iyya 2 sun bayyana
Da duminsa: PDP ta rabu gida 2, sabbin shugabannin jam'iyya 2 sun bayyana. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jam'iyya ta yi sabbin shugabanni

Sakamakon hakan ne mataimakin shugaban jam’iyyar na bangaren kudu, Elder Yemi Akinwonmi, ya baje kafada a kan shi ya fi cancanta ya shugabanci jam’iyya.

Kara karanta wannan

2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar

Sannan mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa, Sanata Suleiman Nazif, yace sai dai duk badakalar da za a yi a yi ta don shi ya fi cancantar kujerar, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Tuni mabiya bayan Nazif suka sanya ranar taron jam’iyyar ya zama ranar Juma’a, 27 ga watan Augusta don yin taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar na kasa wanda ake kira da (NEC).

Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno

A wani labari na daban, jami’an MNJTF sun ragargaji ‘yan bindiga 4 a wani karon batta da suka yi wuraren tafkin Chadi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce Kanal Muhammad Dole, shugaban fannin watsa labaran MNJTF, ya fitar a ranar Litinin a Maiduguri jihar Borno, ta ce sun samu nasarar kwato miyagun makamai daga hannun ‘yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a kwace mulki a hannun Buhari a 2023

Sakamakon kara kaimi da sojoji suka yi sun samu nasarar ragargaje mayakan Boko Haram da na ISWAP wuraren tafkin Chadi.

Rundunar MNJTF yanki na uku na Monguno sun yi zagaye wuraren Gajiram, kwatsam suka gamu da mayakan Boko Haram da na ISWAP sun kai hari wuraren Gambari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel