IGP ya bullo da sabbin hanyoyin maganin 'yan bindiga a jihar Zamfara

IGP ya bullo da sabbin hanyoyin maganin 'yan bindiga a jihar Zamfara

  • Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Baba, ya kawo sabuwar hanyar kawo karshen rashin tsaro a jihar Zamfara
  • Mataimakinsa, AIG Zone 10 na Sokoto, Ali Janga ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara Zamfara a kan matsalar rashin tsaro
  • A cewarsa, IGP ne ya umarce shi da ya zauna da jami’an tsaro don su tattauna akan ayyukan dan sanda akan harkar tsaron kasa

Zamfara - Sifeta janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Baba ya kawo sabuwar hanyar kawo karshen rashin tsaron da jihar Zamfara take fuskanta.

AIG na Zone 10 na jihar Sokoto, Ali Janga ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara a kan wannan rashin tsaron da jihar ta ke fuskanta, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

IGP ya bullo da sabbin hanyoyin maganin 'yan bindiga a jihar Zamfara
IGP ya bullo da sabbin hanyoyin maganin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Hoto daga Channelstv.com
Asali: Facebook

Yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da ‘yan sanda da yayi a Gusau, AIG ya ce IGP ya sauya hanyar kawo karshen rashin tsaron da jihar Zamfara da sauran jihohi suke fuskanta.

Na zo nan bisa umarnin IG don in tattauna da jami’an hukumar dan sanda a kan ayyukansu.
Mun samu wata sabuwar hanyar gyara tsaro a jihar. Za mu hada kai ne da sauran jami’an tsaron wasu jihohi don kawo karshen rashin tsaron da ake fuskanta,”cewar Janga.

Daily Nigerian ta wallafa cewa, AIG ya umarci jami’an hukumarsu da su kasance masu kwazo da dagiya sannan su zama cikin shiri a ko yaushe.

AIG ya kai wa sarkin Gusau ziyara, Alhaji Ibrahim Bello, inda ya nemi goyon bayan shugabannin gargajiya wurin kawo karshen ‘yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga sun dakatar da shigar da man fetur garin Dansadau da makwabtansa tun bayan banka wa wata tankar mai da ta taho daga Gusau zuwa Dansadau wuta.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tankar daya ce daga cikin sauran ababen hawan da jami’an tsaro dauke da makamai suka raka garin Dansadau a ranar Talata, kwatsam kuma sai ‘yan bindigan suka bude mata wuta.

Mai tankar, Alhaji Yau Muhammad Dansadau ya bayyana wa Daily Trust cewa, tun daga gidan man NNPC dake Gusau tankar take don samar da man fetur a garin sakamakon rashin mai wanda ya janyo aka rufe gidajen mayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng