An tabbatar da yadda ‘Yan bindiga suka samu damar shiga makarantar NDA cikin dare

An tabbatar da yadda ‘Yan bindiga suka samu damar shiga makarantar NDA cikin dare

  • Takardar sirri ta tona hanyar da ‘Yan bindiga suka bi, suka shigo har NDA
  • Hedikwatar tsaro ta tabbatar cewa ‘Yan bindigan sun biyo wata katanga ne
  • Bayan sun gama ta’adin, Miyagun sun tsere sun shiga jejin Afaka ko Igabi

Abuja - Wata takardar sirri da ta fito daga hedikwatar tsaro na kasa ta yi bayanin yadda ‘yan bindiga suka shiga makarantar sojoji ta NDA, suka yi barna.

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya bayyana cewa ana tunanin ‘yan bindigan sun shigo makarantar ne ta wani sashe na katanga mara kyau.

Ta titin zuwa filin jirgin sama na Kaduna da ke Afaka, akwai bangaren katangar makarantar sojojin na NDA da shingen da aka sa na wayoyi suna rawa.

Takardar da aka fitar a boye ya gaskata rahoton da jaridar ta fitar a baya, inda ta ce ‘yan bindigan sun yi amfani da jejin da ke kewaye da katangar wajen tsere wa.

Ta bayan rukunin gidajen sojojin da ke cikin makarantar, jeji ne da mutum zai iya bi ba tare da an lura ba.

Abin da jami’an tsaron suka tabbatar da kansu shi ne ‘yan bindigan sun bi ta inda tsaro ya yi sakwa-sakwa, suka samu damar shigo wa makarantar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makarantar NDA
Sashen wata katanga a NDA Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Binciken da aka yi, ya nuna cewa ‘yan bindigan za su ci karo da titin zuwa filin jirgin sama ta wata gona da ke kusa da kauyen Gidan Gado a Afaka.”
“Ana tunanin ‘yan bindigan sun tsere ne ta Buruki ko ta Maguzawa, ko kuma ta yankin Riyawa da ke Igabi, wanda sanannen mafakar ‘yan bindiga ne.”

“Bayan haka, akwai bukatar a share duk wuraren da ke wannan yanki. Ko da yake sauran jami’an tsaro a jihar suna kokarin ceto jami’in da aka dauke.”
“Ana bada shawara cewa akwai bukatar ayi wa tsarin tsaron NDA garambawul gaba daya, domin a hana auku war irin wannan lamari a nan gaba.”

Da walakin abin da ya faru a NDA?

A ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, 2021, aka ji cewa fadar Shugaban kasa ta yi magana game da abin da ya faru a makarantar NDA duk da tsaron da ake da shi.

Garba Shehu yana ganin kamar ‘Yan siyasa na neman bata sunan Gwamnatin Muhammadu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel