Zargin takardun bogi: Kotu ta ki kwace kujerar mai magana da yawun majalisar wakilai

Zargin takardun bogi: Kotu ta ki kwace kujerar mai magana da yawun majalisar wakilai

  • Babbar kotun jihar Abia ta yi fatali da karar da Okey Ezeala ya mika a kan dan majalisar wakilai Benjamin Kalu
  • Ezeala ya zargi Kalu a kan amfani da takardun makaranta na bogi, inda aka zargi akwai sauyin suna a takardun
  • A hukuncin da alkalin Justice A.O. Chijioke ya yanke, ya yi watsi da karar inda yace soki burutsu ne karatun tsuntsaye

Abia - Babbar kotun jihar Abia ta yi fatali da karar da Okey Ezeala ya mika a kan kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu. Ezeala ya zargi Kalu da amfani da takardun makaranta na bogi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai karar ya yi ikirarin cewa akwai canjin suna a takardun makarantarsa.

A wani hukunci da alkali A.O. Chijioke ya yanke, ya ce zargin da ake yi wa Kalu bashi da tushe balle makama.

Kara karanta wannan

Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

Zargin takardun bogi: Kotu ta ki kwace kujerar mai magana da yawun majalisar wakilai
Zargin takardun bogi: Kotu ta ki kwace kujerar mai magana da yawun majalisar wakilai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Justice Chijioke ya yarda da cewa surutan da ake yi a kan Benjamin Kalu duk an yi ne kafin zabe, lamarin da ya musanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta amince da cewa Kalu ya bi duk wasu hanyoyin sanar da hukuma yadda ake canja suna kuma mai kai karar ya kasa kawo wani kwakkwaran hujja don jingana zarginsa da shi.

Kotun ta amince da KC Nwufor, lauyan Kalu, inda yace mai kai kara bai gabatar da asalin mai kwalayen makarantar ba wanda ake zargin Kalu da amfani dasu , Daily Trust ta ruwaito.

A shari’ar da akayi sa’a daya da rabi ana yin ta, kotu ta musanta duk wasu abubuwa da mai kara yake zargin wanda yake kara dasu.

Bayan fatali da karar, kotu ta yanki wani kudi wanda tace wanda ya mika karar zai biya shi.

Kara karanta wannan

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

Bayan yanke hukuncin, Kalu yace:

Kamar yadda nake cewa, Ubangiji adali ne. Kuma a matsayi na na mai imani, na yarda da cewa ba zai taba bari a cuce ni ba.
A matsayina na masanin doma, na yarda da cewa kotu za ta yi min adalci saboda gaskiya ta yi halin ta.
Na yarda da adalcin shari’a tun lokacin zabe. Don haka na yarda kotu za ta yi min adalci ba zan ji kunya ba. Na gode wa mabiya na wadanda suka tsaya a kaina kuma suka nuna min so a wannan lokaci.
Shekaru biyu kenan ina shige da fice a kotu. Abinda yasa suke yin haka don su dauke hankalina a kan ayyukan da nake yi wa mutanen Bande ne, amma na ki yarda hakan ta faru.

Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci

A wani labari na daban, wata mata a jihar Kano ta shiga hannun 'yan sanda sakamakon kama ta da laifin garkame dan ta mai shekaru 12 da tayi tare da hana shi abinci na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Daily Trust ta wallafa cewa, Maryam Dauda ta shiga hannun 'yan sandan jihar Kano ne bayan an kama ta laifin garkame dan ta a wani daki a gidan da suke a Unguwar Liman Dorayi dake karamar hukumar Gwale ta jihar ba tare da bashi abinci ba da kuma kula da lafiyarsa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa har yanzu matar tana hannunsu kuma za a gurfanar da ita nan babu dadewa bayan an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel