Da Ɗumi-Ɗumi: Hoto ya bayyana a yayin da gwamnonin APC biyu suka ziyarci Tinubu a Landan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hoto ya bayyana a yayin da gwamnonin APC biyu suka ziyarci Tinubu a Landan

  • Gwamnonin Jam'iyyar APC, Kayode Fayemi da Rotimi Akeredolu sun ziyarci jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu a Landan
  • Gwamnan jihar Ekiti, Fayemi, ya wallafa hotonsa da gwamnan jihar Ondo da Tinubu a Facebook
  • Tun da farko, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu da wasu mutanen sun ziyarci Tinubun a Landan

Landan, UK - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwarsa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu sun ziyarci jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a Landan, Burtaniya.

Gwamna Fayemi, cikin wani rubutu da ya wallafa a Facebook yace shi da Akeredolu sun ziyarci jigon na APC ne a ranar Laraba 25 ga watan Agusta.

Da Ɗumi-Ɗumi: Hoto ya bayyana a yayin da gwamnonin APC biyu suka ziyarci Tinubu a Landan
Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da takwararsa na Rotimi Akeredolu na jihar Ondo yayin da suka ziyarci Bola Ahmed Tinubu a Landan. Hoto: Kayode Fayemi
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya koka, masu rike da madafan iko sun haramta masa ganin Shugaba Buhari

Ya rubuta cewa:

"Na ziyarci tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu."

A cewar PM News, an yi wa Tinubu tiyata ne a gwiwarsa a Landan kuma yana samun sauki.

Baya ga Fayemi da Akeredolu, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, tunda farko ya ziyarci Tinubu a watan Yuli, a lokacin da ya ce shugaban na APC yana cikin koshin lafiya.

Shugaba Muhammadu Buhari shima ya kai wa Tinubu ziyara a Landan inda suka dauki hotuna da dama.

Tinubu ya yi wa Buhari godiya bisa kai masa ziyara

Tunda farko, Legit.ng ta ruwaito cewa Tinubu ya mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari bisa ziyarar da ya kai masa a Landan.

Sanarwar da hadiminsa ya fitar a ranar Juma'a 13 ga watan Agusta ta ce ziyarar da shugaban kasar ya kai wa Tinubu ya nuna cewa shi mutum ne mai kulawa da mutane.

Kara karanta wannan

APC: Rigimar Ministan harkokin gida da Gwamna ya yi kamari, an sheka da magoya-baya kotu

Ka Ji Kunya: Sadaukin Shinkafi ya soki Mataimakin Gwamnan Zamfara kan ƙin sauya sheƙa zuwa APC

Tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode (Sadaukin Shinkafi) ya yi wa Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Gusau, wankin babban bargo a kan kin komawa jam’iyyar APC.

A wata wallafa da Tsohon ministan yayi ta shafinsa na Twitter, wanda shi din jigo ne na jam’iyyar PDP, ya ce Mahdi bai nuna da’a ba ga gwamnansa, Bello Matawalle, wanda ya canja sheka daga PDP zuwa APC, premium times ta ruwaito.

Gwamnan jihar Zamfara tare da ‘yan majalisar jihar da sauran kwamishinonin jihar sun koma jam’iyyar APC a watan Yuli, bayan watanni kadan da gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da David Umahi na jihar Ebonyi suka koma jam’iyya mai mulkin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel