Gwamnan PDP ya koka, masu rike da madafan iko sun haramta masa ganin Shugaba Buhari

Gwamnan PDP ya koka, masu rike da madafan iko sun haramta masa ganin Shugaba Buhari

  • Gwamna Samuel Ortom yace sam bai isa ya hadu da Muhammadu Buhari su tattauna ba
  • Watakila yawan caccakar Gwamnatin Buhari ta sa Gwamna Ortom bai iya zuwa Aso Villa
  • Ortom ya na zargin Gwamnatin Tarayya da fifita gwamnonin APC wajen ba jihohi bashi

Makurdi - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom yace an dade da haramta masa ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto a ranar Talata, 24 ga watan Agusta, 2021, inda aka ji Mista Samuel Ortom yana cewa an hana shi ganin shugaban Najeriya.

Samuel Ortom yace bai da damar da zai zauna da mai girma Muhammadu Buhari, su tattauna kan batun rashin tsaro domin jin hanyar da zai kawo zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya tada Lauyoyi, yana maganar shigar da Shugaba Buhari gaban kotu

Da yake jawabi, Gwamna Ortom ya zargi na kusa da shugaban kasar da yi masa wannan katangar, yace don haka ya koma aika duk sakonsa ta kafofin watsa labarai.

Rahoton ya nuna Ortom ya zargi kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da daukar dawainiyar makiyayan da suke kai hari, suna yi wa mata fyade a jihar Benuwai.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, gwamnan ya zargi Miyetti Allah Kautal Hore da hannu wajen fatattakar mutum miliyan 1.5 daga Benuwai.

Gwamnan Benuwai
Gwamnan Benuwai Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Ba a yi wa jihohin PDP adalci

“Lokacin da na zama gwamna a 2015, na iske bashin N70bn, na rubuta takarda ga shugaban kasa, aka ba Benuwai aron N28bn, wanda muke biyan mutane yanzu, amma yanzu jihohin APC kadai shugaban kasa yake tura wa kudin.”

Kara karanta wannan

Ahmad Joda bai taba neman alfarma waje na ba, Shugaba Buhari

Ortom yace sukar Muhammadu Buhari bai nufin kiyayya ga Fulani domin ya yaba da kokarin da irinsu Shehu Shagari da Umaru Musa Yar’Adu suka yi a mulki.

Baya ga sukar Buhari, Ortom yace har yau ba a sake jin komai kan wadanda suka nemi su kashe shi ba.

An yi hira da Gwamnan ne domin jin ta bakinsa a kan hanyoyin kiwon dabbobi da gwamnatin tarayya ke kokarin dawo da su, yana ganin hakan ya saba doka.

A makon nan ne aka samu labari cewa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom yace zai iya shiga kotu da mai girma shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.

Ortom yace zai kai shugaban Najeriya kotu idan ya hakikance a kan dawo da labobin kiwon dabbobi domin dokar kasa ba ta yarda da wannan matakin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel