Majalisar Dinkin Duniya ta tono sirrin Gwamnatin Tarayya wajen kawo karshen yakin Boko Haram
- Gwamnatin Tarayya ta shigo da wani tsari na sulhu da ‘Yan ta’adda a boye
- Tsofaffin Sojojin Yan ta’adda da suka tuba suna samun yin sabuwar rayuwa
- Hukumomi na ba tsofaffin ‘Yan Boko Haram gidaje da hanyar neman abinci
Wani rahoto da majalisar dinkin Duniya ta fitar ya yi bayani a kan shirrin sirrin sulhu da gwamnatin tarayya ta fito wa ‘yan Boko Haram da shi.
The New Humanitarian ta yi bincike
Arirse TV ta ce gwamnatin Najeriya ta kawo tsari na musamman da zai sa Boko Haram da sojojin ISWAP su daina fada, sai a samar masu da ayyukan yi.
An fitar da wannan rahoto ne a lokacin da sojojin Boko Haram da na kungiyar ISWAP sama da 1, 200 suka ajiye kayan yaki a ‘yan kwanakin bayan nan.
This Day ta ce The New Humanitarian ta gudanar da bincike domin gano abin da ya sa ‘yan ta’addan suke mika kansu, kuma an gano abin da ya faru.
Ana lallabar 'Yan ta'adda, su mika wuya
Binciken wata shida da aka yi ya nuna hukumomin Najeriya suna tuntubar jagororin ‘yan ta’addan, suna ba su kwarin gwiwar su ajiye makamai.
Lamarin ya kai daga cikin wadanda suka jagoranci kisan daruruwan mutane a Bama a 2014, akwai wanda yanzu yake yawo a gari, ana biyansa albashi.
Jaridar ta ce wani tsohon sojan Islamic State of West Africa Province da ya ajiye makamansa, ya na zaune hankalinsa kwance a yau, ya shiga sabuwar rayuwa.
Ta hannun irinsa da suka tuba ake karkato da ra’ayin sauran mayakan Boko Haram, su ajiye kayan fada.
Tubabban mayakin ya auri wata takwararsa, tsohuwar ‘yar Boko Haran, suna zaune a gida kyauta a garin Kaduna, kuma DSS ta na ba shi na-kashewa duk wata.
Babu wani jami’in gwamnati da zai bude baki ya yi wa Duniya bayani kan wannan tsari na Sulhu da aka shigo da shi duk da ana cin nasara a kan ‘yan ta’addan.
Wannan tsari na Sulhu da ke karkashin kulawar DSS da sojoji, ya sha ban-bam da Operation Safe Corridor domin kananan ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.
Meyasa ake yi wa 'Yan ta'adda afuwa?
Sojoji sun yi bayanin dalilin karbar tubabbun 'yan ta'adda, sun ce yarjejeniya duniya da Najeriya ta sa wa hannu ba ta yarda a kashe 'yan ta'adda da suka tuba ba.
Kakakin rundunar sojojin kasa, Birgediya-Jana Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a wata hira.
Asali: Legit.ng