Yadda Sojojin da ke sa ido ta CCTV suka shararara barci, ‘Yan bindiga suka shiga NDA
- Sakacin ma’aikata ya taimaka wajen kai hari a makarantar sojoji ta NDA
- Barci ya dauke Jami’an da ke dakin lura da na’urorin CCTV a daren yau
- Hakan ya ba ‘Yan bindiga dama suka shigo ta sashen da ba a katange ba
Kaduna - Rahotanni na cigaba da shigo wa game da yadda ‘yan bindiga suka samu damar shiga makarantar koyon aikin soja na NDA da ke garin Kaduna.
Masu kallon CCTV sun yi barci
Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa jami’an tsaron da ke aiki a dakunan da ake sa ido kan na’urorin CCTV na makarantar, sun buge da barci da daddare.
Ta na’urorin daukar hoto na closed-circuit television wanda aka fi sani da CCTV ne ake ganin duk abin da yake faruwa daga wani daki na musamman a gefe.
Rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana cewa barci ne ya ci karfin wadanda ya kamata su rika sa idanu.
Ya abin ya faru?
Wata majiya daga jaridar ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo makarantar sojojin ne ta wata faka da ba a tsaida katanga ba, hakan ya sa suka shigo a boye.
Wani jami’in tsaro ya yi karin bayani, yake cewa ‘yan bindigan sun zo ne da tsakar dare, yace barci ya dauke duk ma’aikatan da suke kula da na’urorin CCTV.
“A cikin tsakar dare ne, ma’aikatan da ya kamata a ce suna lura da CCTV sun buge da barci”
“Ba don haka ba, da sun sanar da kowa, a hana aukuwar lamarin.”
Hukumomin gidan soja za su dauki tsattsauran mataki kan jami’an da suka yi sakacin da ya jawo aka rasa jami’an tsaro, aka kuma yi garkuwa da wani babban soja.
A ka’idar aikin gidan soja, ana hukunta duk wani jami’in da ya saba doka ne a cikin gida, ba tare da an shiga kotun da aka saba gurfanar da gama-garin al’umma ba.
Mutane suna sayen makamai
Kun samu rahoto cewa yawan hare-haren ‘yan bindiga ya jawo al’umma suna daukar bindogi da makamai. Hakan na zuwa ne bayan kiran da wasu gwamnoni ke yi.
Al’umma na tara makaman da za su iya tsare ransu da dukiyoyinsu a jihohin Zamfara, Katsina Kaduna, Neja, da Filato, saboda jami'an tsaron sun gaza kare mutane.
Asali: Legit.ng