Ku binciki hanyar samun kwastomomin ku, EFCC ga bankuna
- EFCC ta umarci bankuna a kan su dinga bincika hanyoyin samun kudaden abokan harkokinsu
- Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya yi wannan furucin a ranar Talata bayan ACAEBIN ya kai masa ziyara Abuja
- A cewar Bawa, wasu masu adana kudade a banki suna samun makudan kudade bayan makwanni 2 da bude asusu
FCT, Abuja - Shugaban EFCC ya umarci bankuna a kan bincike hanyoyin samun kudaden abokan harkokin su.
Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC ya furta hakan a ranar Talata lokacin da ACAEBIN ya kai masa ziyara har Abuja.
Kamar yadda The Cable ta wallafa, Bawa ya ce akwai abokan huldar banki da makudan kudade za su shiga asusunsu cikin watanni biyu da bude asusun bankin.
Zan shawarce ku a kan sanin abokan huldar su, ku san hanyoyin samun kudadensu kafin a bude musu asusu saboda wasu suna bude asusu cikin makonni biyu za ku ga makudan kudade suna shiga asusun, akwai bukatar ku yi kokarin ganin kun samo labarai a kan asusan da wadanda suke da hadi da su,” a cewarsa.
EFCC ta ce kwanan nan za ta fara kama bankuna da laifin barayin yanar gizo da suke dankara kudadensu a asusan bankuna.
Bawa ya shawarci masu kididdiga a bankuna a kan su dage wurin yin ayyuka tukuru a kan hakan, inda yace daga ranar 1 ga watan Satumban 2021, hukumar EFCC za ta koma damkar bankuna indai matsalar kudi ne a asusai,” kamar yadda aka yanko maganar shugaban EFCC din a takardar.
A bangarensa, Uduak Udoh, mataimakin kungiyar ya ce, abokan huldar bankuna suna hada kai da ma’aikatan bankunan ne wurin yasar kudade, ya bukaci taimakon hukumar.
Wasu abokan huldar bankuna suna hada kai ne da ma’aikatan wurin yasar kudade. Muna son ku kalli anguwanni, ba bankuna kadai ba. A shirye muke da mu baku hadin kan da kuke bukata; muna so ku yarda da masu kididdigar bankuna kuma a shirye muke mu samar muku da labarai saboda ba za mu bi bayan ma’aikatanmu marasa gaskiya,” a cewarsa.
A watan Maris ne hukumar EFCC ta umarci duk ma’aikatan bankuna a kan kowa ya bayyana dukiyoyinsa wanda hakan yana cikin hanyar sanin ko ma’aikatan suna tara halastacciyar dukiya, The Cable ta wallafa.
Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi
A wani labari na daban, sabbin labarai sun bayyana na yadda majalisar jihar Kebbi ta tsige kakakinta Ismaila Abdulmumuni Kamba da mataimakinsa, Buhari Aliero.
Daily Trust ta ruwaito cewa, da safiyar Talata ne aka shiga har ofishin kakakin majalisar inda aka sace sandar majalisa wacce ita ce alamar karfin ikon majalisar.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa sauran 'yan majalisar sun dauke sandar ne domin tabbatar da tsige manyan majalisar. Daga nan ne suka zauna bayan dauke sandar a can wani wuri da ba a sani ba inda suka tsige shi.
Asali: Legit.ng