Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi

Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi

  • An gano cewa, 'yan majalisa sun sace sandar majalisa daga ofishin kakakin majalisar inda suka tafi da ita can wani wuri suka tsige shi
  • Sun bayyana ne a zauren majalisar inda magatakardan majalisa ya bayyana sunan sabon kakakin majalisa da mataimakinsa
  • Magatakarda Ahmed Usman Bunza, ya sanar da cewa mutum 21 daga cikin 24 na 'yan majalisar ne suka amince da tsige shugabannin

Kebbi - Sabbin labarai sun bayyana na yadda majalisar jihar Kebbi ta tsige kakakinta Ismaila Abdulmumuni Kamba da mataimakinsa, Buhari Aliero.

Daily Trust ta ruwaito cewa, da safiyar Talata ne aka shiga har ofishin kakakin majalisar inda aka sace sandar majalisa wacce ita ce alamar karfin ikon majalisar.

Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi
Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa sauran 'yan majalisar sun dauke sandar ne domin tabbatar da tsige manyan majalisar. Daga nan ne suka zauna bayan dauke sandar a can wani wuri da ba a sani ba inda suka tsige shi.

Kara karanta wannan

An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar

A zauren majalisar, magatakarda Ahmed Usman Bunza ya sanar da sunan dan majalisa mai wakiltar mazabar Bagudo, Muhammed Abubakar Lolo a matsayin sabon kakakin majalisar da kuma Mohammed Usman Zuru a matsayin mataimakin majalisar.

Dan majalisa mai wakiltar Fakai a jihar Kebbi, Lawal Haruna Gele, shine ya mika bukatar tsige mataimakin majalisar.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Muhammed Tukur, ya ce 'yan majalisa uku kacal daga cikin ashirin da hudu ne suka ki saka hannu kan bukatar tsige shugabannin majalisar.

'Yan majalisa ashirin da daya daga cikin ashirin da hudu ne suka saka hannu kan bukatar tsigesu. Babu wanda ya rinjayi hukuncinmu," yace.

Tuni dai an rantsar da sabon kakakin majalisa da mataimakinsa.

A lokacin da aka tuntubi tsohon shugaban majalisar ko zai yi tsokaci kan wannan lamarin, ya ce "Ba zan yi magana ba yanzu."

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Jihar Zamfara ta samu sabon Shugaban Ma'aikata

'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga sun dakatar da shigar da man fetur garin Dansadau da makwabtansa tun bayan banka wa wata tankar mai da ta taho daga Gusau zuwa Dansadau wuta.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tankar daya ce daga cikin sauran ababen hawan da jami’an tsaro dauke da makamai suka raka garin Dansadau a ranar Talata, kwatsam kuma sai ‘yan bindigan suka bude mata wuta.

Mai tankar, Alhaji Yau Muhammad Dansadau ya bayyana wa Daily Trust cewa, tun daga gidan man NNPC dake Gusau tankar take don samar da man fetur a garin sakamakon rashin mai wanda ya janyo aka rufe gidajen mayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel