Ana zargin Shugaban Majalisa da karbar cin hancin Naira Biliyan 4 domin ya canza zubin PIB

Ana zargin Shugaban Majalisa da karbar cin hancin Naira Biliyan 4 domin ya canza zubin PIB

  • Ahmad Lawan yace babu wanda aka ba cin hanci domin a taba kudirin PIB
  • Shugaban majalisar yayi watsi da rade-radin cewa sun lakume Miliyan $10m
  • Lawan ya gargadi jama’a a kan yin magana ba tare da suna da wata hujja ba

Da gaske an ba 'Yan majalisa cin hanci?

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Ahmad Ibrahim Lawan ya musanya zargin cewa ya karbi kudi domin ya yi kwaskwarima a cikin kudirin PIB.

Ana jita-iitar cewa an ba Sanata Ahmad Ibrahim Lawan cin hancin Dala miliyan 10 da nufin a jirkita kudirin PIB wanda ya zama doka a kwanaki.

Ahmad Lawan yace daga shi har shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da sauran ‘yan majalisa, babu wanda aka ba cin hanci.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Premium Times ta ce Lawan ya bayyana wannan a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, 2021, bayan ya hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dr. Lawan ya maida martani ne a kan jita-jitar cewa sun karbi rashawa wajen aiki kan kudirin PIA, wada hakan ya fusata wasu ‘yan majalisar kasar.

A lissafin canjin kudin waje a yau, dala miliyan 10 ya haura Naira biliyan hudu a kudin mu na gida.

Shugaban Majalisa
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jaridar ta ce zargin da ake yi wa ‘yan majalisar tarayyar shi ne sun rage kason abin da za a rika ba garuruwan da ake harko danyen mai a kasarsu a kudirin.

Wannan sashe ya kawo hayaniya a majalisa, yayin da wasu suke ganin ya kamata a ware wa al’ummar da aka hako mai a wajensu 5%, sai aka kare a 3%.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

Wani bangare da ya jawo surutu a PIA shi ne 30% na ribar da NNPC ta samu da za a rika raba wa.

Mutane su iya bakinsu - Lawan

Shugaban majalisar yace labarin ba gaskiya ba ne, babu dalilin yada shi, kuma bai da madogara. Har ila yau, ya ja kunnen mutane kan yadda ake amfani da FOI.

“Mutane suna fadan duk abin da suka ga dama a kan shugaban kasa, ‘yan majalisa, su kira mu da sunaye, wannan ya na cikin farashin shiga siyasa."

Sauye-sauyen PIB

Sabuwar dokar PIA ta kawo gyara a harkar man fetur ta yadda mu ka ji cewa ba kowa zai iya shigo da mai daga kasar waje ba sai yana da matatar da ke tace man.

A baya akwai wasu masu lasisin zuwa kasashen ketare, su dauko mai zuwa Najeriya. Daga ciki har da kamfanin Dangote Oil Refinery Company da takwaransa, BUA.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng