Hotunan katafaren gidan Prince Harry da Meghan Markle da aka narka N81.9bn wurin gina shi
- Martani daban-daban daga jama'a sun dinga zuwa bayan bayyanar hotunan katafaren gidan Duke da Duchess din Sussex, Yarima Harry da Meghan Markle ke rayuwa
- Kamar yadda aka gano, an narka N81.9 biliyan wurin gina katafaren gidan mai tsarika daban-daban wanda ya hada da wuraren cin abinci kala-kala
- Yayin da jama'a ke ta jinjinawa ma'auratan kan tsarin da salon rayuwarsu, wasu na ta fatan Allah ya mallaka musu irin wannan katafaren gidan
Montecito, California - Bayan watsi da al'amuran sarauta da ma'auratan suka yi, Duke da Duchess din Sussex, Yarima Harry da Meghan Markle sun koma katafaren gidansu wanda ya ja hankulan jama'a.
Bayyanar hotunan katafaren gidan na alfarma ya janyo cece-kuce daga jama'a a kafar sada zumunta.
Kamar yadda Home Junkie ta wallafa hotunan katafaren gidan a shafinta na Facebook, an kashe $19.9 miliyan wanda yayi daidai da N81.9 biliyan wurin gina shi.
Tabbas tsarin gidan yayi kyau da na sarauta da kuma jinin sarauta, yana da kalar ruwan madara a ciki da kuma bangon shi mai yanayin biskit.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An gano cewa katafaren gidan yana da wuraren cin abinci masu yawa da aka yi wuri daban-daban na gidan tare da wuraren wanka biyu.
Wikipedia ta ruwaito cewa ma'auratan sun angwance ne a shekarar 2018 kuma sun haifa 'ya'ya biyu a halin yanzu.
Kafar sada zumunta sun yi martani
Alicia Jolanta Kubala ta ce:
Ban ga dakunan yara ba. Na ga mai kalar hoda amma babu gadon yara, babu kayan wasansu. Yanayin kayan dakin sun bani mamaki, zaton zan gansu na zamani. Amma me na sani? Kila wannan hotunan kafin su tare ne.
Margaret Reimer ta rubuta:
Me zai sa jama'a ba zasu bar su haka ba. Harry yana da kudi, don haka yana da damar yin irin wannan gidan.
Peggy Reinbold-Wasson tsokaci yayi da:
Ku yarda kawai, babu yadda za a yi ta iya gina wannan katafaren gidan da bata aura Harry ba.
Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF
A wani labari na daban, Manjo janar Abdul-Khalifah Ibrahim, kwamandan sojojin MNJTF ya bukaci rundunonin soji da su shirya ragargazar ragowar mayakan Boko Haram da suke wuraren tafkin Chadi.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Juma’a, Shugaban fannin yada labaran soji na MNJTF, Kanal Muhammad Dole ya ce Ibrahim yayi wannan maganar ne a lokacin da ya zagaya sansanonin sojojin yankin.
Dole ya ce a makon da ya gabata kwamandan ya kai ziyara bangare na uku dake Monguno a Najeriya, bangare na daya dake Moura a Kamaru da bangare na boyu dake Bagasola a Chadi.
Asali: Legit.ng