Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

  • Hadi Sirika ya gabatar da wasu takardun neman kwangila a gaban Majalisar FEC
  • Ministan harkokin jirgin saman yace duka takardunsa sun samu shiga a taron jiya
  • Daga ciki an amince masa ya batar da Naira miliyan 650 a wajen shigo da karnuka

Buhari ya halarci zaman FEC

Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa, FEC, ta amince a batar da Naira miliyan 658 domin sayen karnuka na musamman da ake amfani da su a filin jirgi.

Jaridar The Cable ta ce majalisar ta amince da wannan ne a wajen taron mako-mako da ta saba yi duk ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke garin Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagaoranci zaman jiya, wanda shi ne na farko tun bayan dawonsa Najeriya daga Ingila inda ya shafe kwanaki 18.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Takardun Hadi Sirika sun samu shiga

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika, ya bayyana wannan cigaba da ake samu lokacin da ya zanta da manema labarai bayan taron a fadar Aso Villa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa majalisar FEC ta amince da takardu hudu da ma’aikatarsa ta gabatar, aka amince masa ya kashe N16, 697, 742, 839.

“FEC ta amince takardu hudu daga ma’aikatar jiragen sama. Daga ciki akwai bukatar gina filin jirgin Wachakal a Yobe da zai ci kudi, N6, 284, 065, 056.”

Shugaba Buhari ya yarda a sayo karnuka
Irin Karnukan da ke binciken kaya a filin jirgi Hoto: www.sfgate.com
Asali: UGC

A cewar Mai girma Ministan, za a kashe wadannan kudi ne wajen yin wasu ayyuka a fadin kasar nan.

Za a kashe Naira biliyan 6.3 wajen gina filin tashi da saukar jirgin saman Wachakal a jihar Yobe. Sannan akwai wasu ayyukan da za su ci Naira miliyan 219.8.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za ka sani game da rayuwar Marigayi Sanata Mantu da COVID-19 tayi ajalinsa

Ministan yace daga cikin wadannan kudi, za a saye motocin kwana-kwana na maganin gobara na Naira biliyan 9.5, da kuma karnuka na Naira miliyan 658.8.

Za a kashe miliyoyi a kan karnuka?

Za a ajiye wadannan karnuka a filayen jirgin sama na garin Legas da Abuja domin su rika bankado masu yunkurin shigo wa ko fito da miyagun abubuwa.

"Saboda haka za a kashe N658, 762, 783.36 wajen wannan kwangila, an saka 7.5% na kason VAT.”

Ana so a kara wa shugabanni wa'adi

A ranar Laraba aka ji labari cewa an tafi kotu da nufin a ba Muhammadu Buhari da Gwamnoni damar kara zarcewa kan karagar mulki, har su yi wa'adi uku a ofis.

Wani jagoran APC a Ebonyi, Hon, Hon. Charles Oko Enya yana so a ba sauran masu mulki damar fito wa takara fiye da sau biyu kamar yadda 'yan majalisa su ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel