PIA: Gwamnati ta janye damar musamman da aka ba BUA, Dangote su shigo da mai daga waje
- Shugaba Muhammadu Buhari ya soke damar shigo da tacaccen man fetur
- Dokar PIA aka shigo da ita, ta goge damar da aka ba wasu kamfanoni a da
- Yanzu sai wadanda matatarsu ke aiki za su iya kawo mai daga kasar waje
Dokar harkar mai ta PIA da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba wa hannu, ya soke damar da aka ba wasu wajen shigo da mai daga ketare.
The Cable ta ce tun da wannan kudiri ya zama doka, an shafe duk wata damar da aka ba kamfanonin masu zallar lasisin kafa matatun danyen mai.
Wasu kamfanonin abin zai shafa?
Akwai kamfanonin da ke damar shigo da mai daga waje, irinsu Dangote Oil Refinery Company, Waltersmith Refining & Petrochemical Company Limited.
Sai kamfanin OPAC Refineries, Niger Delta Petroleum Resources, BUA Refinery & Petrochemicals da kuma Edo Refinery and Petrochemical Company Limited.
Jaridar ta ce shigo da wannan doka zai canza wa kamfanonin yadda suke tafiyar da kasuwancinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sashe na 317 (8) na dokar PIA ya kayyade wadanda za a iya ba lasisin shigo da mai, wadanda aka ba dama sune wadanda matatunsu sun riga sun soma aiki a kasa.
Kudirin majalisar dattawa na PIB da aka aika wa shugaban kasa ya kawo wannan sashen ne domin a karfafa gwiwar kamfanoni da suke tace mai a gida.
Kamfanonin za su rika shigo da man da aka tace daga kasashen waje domin a cike gibin da ake da shi. Za a ba kowa adadin man da zai kawo, daidai kafinsa.
PIB ya zama dokar kasa a 2021
Rahoton yace a dokar da shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu a ranar 16 ga watan Agusta, sai matatun da suka fara aiki ne za su iya shigo da mai.
Wani sharadin da aka kakaba a dokar PIA shi ne sai wanda ya yi fice a wajen kasuwanci a kasar waje zai samu lasisin dakon tataccen mai daga kasashen ketare.
Ruwa zai yi gyara
NIMET ta fitar da wani jawabi, inda ta ja-kunnen mutane cewa kwanan nan ruwan sama zai jawo ambaliya a tituna, gonaki da gidajen al’umma a kusan duka jihohi.
Hasashen masanan ya nuna sai an yi hattara, domin za a iya samun hadari tsakanin jiya zuwa yau.
Asali: Legit.ng