Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum

Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce ba duk tubabbun ‘yan Boko Haram bane ‘yan ta’adda
  • A cewar gwamnan, fiye da mayaka 2600 ne suka zubar da makamansu kuma da yawansu tuba suka yi ta hakika
  • Zulum ya yi wadannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da Shugaba Buhari a fadarsa ranar Talata

FCT, Abuja - Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce ba duk tubabbun mayakan Boko Haram da suka tuba cikin kwanakin nan ne ‘yan ta’adda ba.

The Cable ta ruwaito cewa, Gwamnan ya ce fiye da ‘yan ta'adda 2600 ne suka yada makamansu, kuma da yawansu sun yi tuba ta hakika.

Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum
Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum. Hoto daga Babagana Umar Zulum
Asali: Facebook

Zulum ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum

Ya bayyana yadda da yawan wadanda suka tuba mata ne da kananan yara wadanda aka tilasta su a kan ta’addanci kuma aka koya musu amfani da AK 47.

Ya kara da bayyana yadda babu wata doka da ta bayar da damar kashe ‘yan ta’adda inda yace za a ba su horo don wasu dalilai.

Ya tabbatar wa wadanda ta’addanci ya shafa inda yace su ma ba za a bar su a baya ba, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya ce an kashe fiye da mutane 100,000 a cikin shekaru 12 da barkewar rashin tsaro a arewa maso gabas.

Hedkwatar tsaro ta ce fiye da ‘yan ta’adda 1000 ciki har da kwamandojin Boko Haram da masu hada bama-bamai suka mika kawunansu ga sojojin Operation Hadin Kai.

Kara karanta wannan

Ku daina miyagun kalamai game da tubabbun ƴan Boko Haram, ku yi musu zaton alheri, FG

Mutane da dama sun caccaki gwamnatin tarayya a kan maganar yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da kuma inganta rayuwarsu don su cigaba da rayuwa cikin al’umma.

Shugaban Majalisar tarayya, Ahmad Lawan ya yi kira ga al’umma akan su rungumi tubabbun ‘yan Boko Haram din kuma su yafe musu.

Lawan ya ce wajibi ne a bi hanyoyin tabbatar da cewa tubarsu ta hakika ce.

Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da rashawa na EFCC a Maiduguri jihar Borno sun kama mutane biyu kan zargin 'asirin samun kudi' a jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

A cewar EFCC, daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Malam Ayu Sugum, ya umurci wani Abubakar Bakura ya sato N2.9m daga wurin wanda ya ke yi wa aiki.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Sugum, da aka gano cewa yana ikirarin cewa yana aiki da iskokai, ya yi wa Bakura alkawarin cewa zai yi masa asiri ta yadda zai zama attajiri cikin kwanaki 14, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel