Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna

Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna

  • A ranar Talata da safe ne wasu miyagun mutane suka harbe wani babban soja mai suna Wulah da wani CM Okonkwo har lahira
  • 'Yan bindigan sun afka har cikin barikin Afaka ta NDA da misalin 1am yayin da sojoji da dama suke ta bacci
  • An samu rahotanni a kan yadda 'yan bindigan suka yi garkuwa da wani Manjo Datong sannan suka ji wa wani daban miyagun raunika

Kaduna - A ranar Talata da sassafe ne wasu 'yan bindiga suka kai farmaki barikin Afaka dake NDA inda suka harbe wani soja mai mukamin Lieutenant Commander mai suna Wulah, da wani Flying Lieutenant CM Okoronwo har lahira.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka afka barikin da misalin karfe 1am.

Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna
Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya daga barikin tace ana zargin wadanda suka kai farmakin sun bari ne daidai lokacin da mutane da dama suke bacci.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Majiyar ta ce, an kara tsananta tsaro don gudun 'yan bindigan su tsere da wadanda suka yi garkuwa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito yadda su ka yi garkuwa da wani Manjo Datong a ranar yayin da suka ji wa wani soja mai mukamin 2nd Lieutenant miyagun raunika sakamakon harbe-harben, yanzu haka yana asibitin NDA ana kulawa da lafiyarsa.

Bai wuci mako guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori shugabannin tsaro ba akan su kara dagewa wurin ganin sun kawo karshen rashin tsaro.

'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Zamfara da wasu jami'ai daga hukumomin tsaro da suka hada da sojoji sun tsananta sintirin sama da kasa a yankin Gusau zuwa titin Tsafe zuwa Yankara dake karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Kara karanta wannan

Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

Akwai rahotannin sirri da suka bayyana cewa 'yan bindiga na barazanar kai hari wasu yankunan karamar hukumar Tsafe dake jihar.

Rundunar tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro ballantana sojojin sun tsananta tsaro a Tsafe da kewaye domin baiwa dukiyoyi da rayuka tsaro,"'yan sandan suka ce.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel