Hoton tsohon soja mai shekaru 96, ƴaƴa 50 da mata takwas da ke safarar wiwi tsawon shekaru 39 a Niger

Hoton tsohon soja mai shekaru 96, ƴaƴa 50 da mata takwas da ke safarar wiwi tsawon shekaru 39 a Niger

  • Jami'an hukumar NDLEA a jihar Niger sun kama wani tsohon soja mai shekaru 96 da ke sayar da wiwi
  • An kama Pa Joseph Owherhi, a gidansa da ke garin Suleja da ke jihar Niger bayan samun bayanan sirri
  • Bayan samun miyagun kwayoyin a gidansa, Owherhi, ya amsa cewa ya fara sayar da kwayar tun 1982 kuma yana da 'ya'ya 50 da mata 8

Suleja, Jihar Niger - Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, sun kama wani tsohon soja mai murabus, Pa Joseph Owherhi, a garin Suleja da ke jihar Niger kan safarar miyagun kwayoyi, Daily Trust ta ruwaito.

Hoton tsohon soja mai shekaru 96, ƴaƴa 50 da mata takwas da ke safarar wiwi tsawon shekaru 39 a Niger
Tsohon soja mai shekaru 96 da aka kama bisa laifin safarar miyagun kwayoyi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kakakin hukumar Femi Babafemi, a ranar Talata a Abuja ya ce an kama tsohon ne a gidansa da ke Rafin Sanyi a Suleja a ranar Asabar, 21 g watan Agusta da kilo giram na wiwi bayan samun bayannan sirri, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magama-Saminaka: An yi kira ga Gwamnatoci su gyara titin da zai sa a daina kashe Matafiya a Jos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ya ce shekarunsa 39 yana safara wiwi

Da aka yi masa tambayoyi, Owherhi, wanda ya amsa cewa laifinsa ya ce ya fara safarar kwayan ne tun lokacin da ya yi murabus daga aikin soja a 1982.

Ya kuma yi ikirarin yana da matan aure 8 da 'ya'ya 50 kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An kama wasu masu fataucin miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje

Har wa yau, NDLEA ta kama wasu mutane hudu da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne zuwa kasashen ketare yayin da suke yunkurin tsallaka iyakar kasar a kan babur a kauyen Kolere da ke karamar hukumar Mubi zuwa Kamaru a ranar Asabar dauke da Tramadol da ake boye cikin katon din taliya.

Babafemi ya ce wadanda aka kama din sun hada da Umar Mohammed, Ibrahim Aliyu, Aliyu Adamu da Usman Adamu.

Kara karanta wannan

An kama hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo a cikin coci a Legas

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel