Magama-Saminaka: An yi kira ga Gwamnatoci su gyara titin da zai sa a daina kashe Matafiya a Jos

Magama-Saminaka: An yi kira ga Gwamnatoci su gyara titin da zai sa a daina kashe Matafiya a Jos

  • Ana kira ga gwamnatoci su gyara titin da ya hada Bauchi da jihar Kaduna
  • Matafiya za su iya bin hanyar Magama Gumau maimakon su shiga Filato
  • Wannan titi zai shigo da mutum Saminaka ba tare da ya aukawa hadari ba

Ibrahim Sule ya yi wannnan rubutu da nufin wayar da kan al’umma game da hanyar Magama Gumau a jihar Bauchi zuwa garin Saminka, jihar Kaduna.

Sule malami ne a jami’ar tarayya da ke garin Maiduguri, Borno, ya yi rubutun ne a Daily Trust.

Marubucin yake cewa idan an karasa aikin wannan titi, za a kare matafiya daga hadarin bin garin Jos.

Jos - Kwanakin baya aka samu wasu miyagu da suka hallaka Bayin Allah a garin Gada-Biyu, karamar hukumar Jos Filato, ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Ba wannan ne karon farko da aka kashe mutane babu gaira babu dalili a yankin ba, tun bayan rikici da ya barke a Jos a 2001, wurin ya yi kaurin-suna da wannan.

Don haka akwai bukatar gwamnati ta yi maza ta shawo kan wannan lamari, kafin ya dauki sabon salo, a hukunta masu laifi, a samar da wata hanyar da za a iya bi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Magama-Saminaka
Titi a Garin Bauchi Hoto: constructionreviewonline.com
Asali: UGC

Marubucin yace a dalilin wannan, ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su gaggauta aikin gyara titin da ya hada jihohin Bauchi da Kaduna.

Magama Gumau zuwa Saminaka.

Idan aka gyara hanyar Magama Gumau zuwa Saminaka, zai taimaka sosai wajen rage wahalar da al’umma ke sha wurin zuwa Arewa maso gabas daga yankin Kudu.

Titin Magama Gumau zuwa garin Saminaka zai fi hanyar Gada-Biyu, garin Jos da ake bi aminci.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Wannan titi zai hada Bauchi da Saminaka, daga nan ya bi ta Zaria, zuwa Kaduna, har Abuja. Hakan zai sa masu zuwa daga Abuja da kewaye, su huta da bi ta Jos.

A karshe, wannan marubuciya yi kira ga hukuma da babban murya, ta yi abin da ya dace wajen hukunta wadanda suka kashe matafiya haka kurum a jihar ta Filato.

FIRS ta kara budi a 2022

Najeriya ta hango karin Naira tiriliyan biyar a kudin shiga saboda za a sa wa kamfanonin waje haraji. FIRS ta ce daga cikin wadannan kamfanoni akwai Twitter.

FIRS ta ce gwamnati za ta kirkiro dabarun zamani domin a rika karbar haraji a kan hanyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel