Babbar Magana: Na Tsallake Harin Yan Boko Haram Sama da 50, Gwamna Zulum

Babbar Magana: Na Tsallake Harin Yan Boko Haram Sama da 50, Gwamna Zulum

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum yace ya tsallake harin yan Boko Haram sama da 50 daga zuwansa mulki
  • Zulum ya kuma kara da cewa bai ga dalilin da zai sa a ki amincewa da yan ta'addan da suka mika wuya ba
  • Gwamnan yace daga fara rikicin Boko Haram zuwa yanzun an kashe jama'ar Borno 100,000

Abuja - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, yace mayakan kungiyar Boko Haram sun kai mishi hari sama da sau 50, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata.

Zulum yace sama da mutum 100,000 ne aka kashe a cikin shekaru 12 da aka kwashe na rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum
Babbar Magana: Na Tsallake Harin Yan Boko Haram Sama da 50, Gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno FB Fage
Asali: Facebook

Gwamnan, wanda ya bayyana cewa adadin yan ta'adda 2,600 suka mika makamansu, ya kara da cewa adadin ya kunshi kananan yara, matan aure da kuma iyalan tsofaffin mayakan Boko Haram.

An tilasta wa wasu shiga Boko Haram

Zulum yace daga cikin waɗanda suka mika wuyan har da waɗanda basu ji ba basu gani ba, waɗanda aka tilastawa shiga kungiyar Boko Haram.

Hakanan yace akwai kananan yara daga cikin masu mika wuyan waɗanda ba su kai doka ta hau kansu ba.

Gwamnati ba zata sakankace da masu mika wuyan ba

Zulum yace gwamnatin jihar Borno ba ta tunanin baiwa yan ta'addan wani gata saboda sun mika makamansu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Zulum yace:

"Mun tattauna lamarin mika wuyan mayakan Boko Haram da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma bana tunanin akwai wani dalili da zaisa aki amincewa da su."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA, sun hallaka Soja 2, sun sace 1

Yan Najeriya sun rarrabu kan yan Boko Haram da suka tuba

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa an samu rarrabuwar kai game da mayakan Boko Haram da suka mika wuya kuma suka nemi gafarar yan Najeriya.

Wasu yan Najeriya na ganin ya kamata a yafe musu tunda sun tuba kuma sun nemi yafiya, yayin da wasu ke ganin ya zama wajibi a hukunta su.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matakin da Ta Dauka Bayan Kotu ta Dakatar da Shugabanta, Secondus

Jam'iyyar PDP ta sanar da ɗage taron kwamitin zartartarwa (NWC) da aka tsara za'a yi yau Talata

Mataimakin shugaban PDP (Kudu), Yemi Akinwonmi, shine ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar. Wannan matakin na PDP ya biyo bayan hukuncin kotu na dakatar da shugaban PDP, Uche Secondus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262