Abubuwa 5 da zai sa a dade ba'a daina magana kan auren Yusuf da Zahra ba
Karshen makon da ya gabata na cike da labaran daurin auren Yusuf Buhari, 'dan shugaban kasa Muhammadu Buhari da 'diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Bayero.
A wannan rahoton, Legit.ng ta tattaro muku dalilai biyar da zasu sa a dade ana magana kan wannan daurin aure.
1. An rabawa mahalarta wayoyin Iphone 12 Pro Max
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an raba kaya masu tsada a matsayin tukwuici ga wadanda suka samu halartar bikin ‘dan shugaban Najeriya.
Kamar yadda hotuna da bidiyoyi suka nuna an raba wani kwali da yake dauke da wayar Iphone da kuma na’urar Ipad, duk na kamfanin Apple, a wajen bikin.
An yi wa wannan kwali tambari da sunayen amarya da ango da ranar aurensu. A ciki za a ga dambareriyar wayar Iphone 12 Pro wanda ake yayi a Duniya.
2. Adadin jiragen da suka dira a Bichi don daurin auren
Akalla jiragen sama na alfarma guda 25 cike da kasaitattun mutane masu fadi aji a fadin Najeriya har da ketare suka dira jihar Kano don shaida daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wakilin Daily Trust ya kirga akalla jiragen sama na alfarma guda 20 da ya gani a filin jirgin Malam Aminu Kano a ranar Juma'a 20 ga watan Agusta da aka daura auren.
3. An cashe da haramtacciyar wakar 'Coming' ta Naira Marley
Duk da cewa hukumar lura da gidajen talabijin da rediyo a Najeriya ta haramta sanya wakar 'Coming' ta mawaki Naira Marley. Hakan ya sa akayi mamakin yadda Amarya da Ango suka cashe da wannan wakar a bikin.
4. Manyan jiga-jigan siyasan da suka hallara
Manyan jiga-jigan siyasan Najeriya akalla 20 sun dira kasar Bichi, a jihar Kano domin halartan daurin auren 'dan Buhari daya tilo, Yusuf, da diyar sarkin Bichi, Zahra Bayero.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ne ya daura aure a Masallacin kasar Bichi.
Daga ciki akwai Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, Ahmad Lawan, Osinbajo, Dantata, Mamman Daura, dss.
5. Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci fitaccen malamin nan, Mufti Menk domin wa'azi yayin da ake liyafar cin abincin rana da ya gayyaci abokai da 'yan uwa domin taya murnar auren dan shi namiji daya tilo, Yusuf Muhammadu Buhari.
Kamar yadda katin gayyatar ya bayyana, an yi liyafar cin abincin ranan ne domin karramawa tare da tarbar amarya Zahra Nasir Bayero.
Babu shakka dakin taro na Banquet dake gidan gwamnatin tarayya ya cika dankam da manyan 'yan siyasa, gwamnoni, ministoci da kuma masu fadi a ji a kasar nan.
Asali: Legit.ng