Atiku, Jonathan, Mamman Daura da sauran manyan da suka dira kasar Bichi don auren 'dan Buhari
Manyan jiga-jigan siyasan Najeriya sun dira kasar Bichi, a jihar Kano domin halartan daurin auren 'dan Buhari daya tilo, Yusuf, da diyar sarkin Bichi, Zahra Bayero.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ne ya daura aure a Masallacin kasar Bichi.
Yayinda babban attajiri, Alhaji Aminu Dantata, ya bada auren a madadin iyalan Sarkin Bichi; dan uwa kuma babban aminin Buhari, Malam Mamman Daura, ya karba aure matsayin wakilin ango kuma madadin shugaba Buhari.
An dade ba'ayi daurin auren da ya tattara manyan masu fada a aji irin wannan ba.
Ga jerin wasu sannannu da suka halarci daurin aure:
1. Shugaba Muhammadu Buhari
2. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
3. Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
4. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
5. Tsohon shugaban kasan jamhurriyar Nijar, Mohammadou Issoufou
6. Alhaji Aminu Dantata
7. Malam Mamman Daura
8. Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje
9. Shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi
10. Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu
11. Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal
12. Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Talamiz
13. Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni
14. Mataimakin gwamnan Kano, Yusuf Gawuna
15. Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
16. Gwamnan Borno, Babagaba Umara Zulum
17. Sanata Ahmad Sani Yarima
18. Sanata Ali Ndume
19. Malam Nuhu Ribadu
20. Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ado Doguwa, da sauransu.
Asali: Legit.ng