Hotuna: Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman

Hotuna: Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman a bikin dan shi namiji tilo
  • Liyafar cin abincin ranan da shugaban kasa ya shirya a gidan gwamnatin tarayya ta samu halartar manyan mutane
  • An yi wannan walima ne domin murna tare da tarbar amarya, Gimbiya Zahra Nasir Bayero zuwa cikin iyalan

Aso Villa, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci fitaccen malamin nan, Mufti Menk domin wa'azi yayin da ake liyafar cin abincin rana da ya gayyaci abokai da 'yan uwa domin taya murnar auren dan shi namiji daya tilo, Yusuf Muhammadu Buhari.

Kamar yadda katin gayyatar ya bayyana, an yi liyafar cin abincin ranan ne domin karramawa tare da tarbar amarya Zahra Nasir Bayero.

Kara karanta wannan

Hotunan shagalin 'Luncheon' na auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero

Babu shakka dakin taro na Banquet dake gidan gwamnatin tarayya ya cika dankam da manyan 'yan siyasa, gwamnoni, ministoci da kuma masu fadi a ji a kasar nan.

Hotuna: Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman
Hotuna: Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman. Hotuna daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari Sallau, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a harkar yada labarai, ya wallafa yadda jiga-jigai da suka hada da shugaban majalisa dattawa, Ahmed Lawan, Sarkin Bichi kuma mahaifin amarya, Alhaji Nasir Ado bayero, matar shugaban kasa, mataimakinsa, matar gwamnan Niger da sauran matan gwamnoni suka cika dakin taro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel