An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar

An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar

  • Majalisar Jihar Zamfara ta dakatar da zamanta saboda sace mahaifin kakakinta
  • Yan bindiga sun sace Alhaji Mua'azu Abubakar ne yayin harin da suka kai a garinsu
  • Majiya daga majalisar ta ce ba za a cigaba da zaman majalisar ba sai an ceto wadanda aka sacen

Majalisar Jihar Zamfara ta dakatar da zamanta har sai baba ta gani saboda sace mahaifin kakakin majalisar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Makonni uku da suka gabata ne yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar bayan kai hari a garinsu na Magarya a yankin Kanwa na karamar hukumar Zurmi.

An dakatar da zaman majalisa a Zamfara saboda sace mahaifin kakakin majalisar
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahaifin kakakin majalisar da aka sace, Alhaji Mua'azu Abubakar shine hakimin Sabon Garon Magarya a yankin Kanwa a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Jihar Zamfara ta samu sabon Shugaban Ma'aikata

Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun kuma sace kishiyoyin mahaifiyar kakakin majalisar yayin da suka kai harin. Kakakin na wakiltar mazabar Zurmi ta Gabas ne a majalisar.

Halin da ake ciki da yan bindigan?

An fara tattaunawa da yan bindigan kuma rahotanni sun ce yan bindigan na ta sauya sharrudan da suke son a cika musu kafin sakin mahaifin kakakin.

Wani shugaban yan bindiga mai suna Halilu Kachalla aka ce shine ke taimakon mahukunta don ganin an ceto mahaifin kakakin da sauran mutanen.

Amma wata kwakwarar majiya ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa majalisar na Zamfara ta dakatar da zamanta bayan afkuwar lamarin.

Majiyar, babban jami'i a majalisar, ya ce yan majalisar sun damu matuka da afkuwar lamarin.

Yaushe za a cigaba da zaman majalisar?

Majiyar ya kara da cewa:

"Akwai bututuwa da dama da ke gaban majalisar kaman maganan tantance zababbun kwamishinoni da wasu abubuwan da aka dakatar sai an sako mahaifin kakakin."

Kara karanta wannan

'Yar musulma ta samu tallafin fasto, mahaifiyarta ta durkusa a coci domin nuna godiya

Majiyar ya kara da cewa an mika musu sunayen zababbun kwamishinonin tun makonni biyu da suka gabata amma sun yanke shawarar ba za su duba batun ba sai an ceto wadanda aka sace.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel