Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure

  • Kyawawan hotunan 'ya'ya mata uku na shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mazansu na aure sun bayyana
  • Sun dauka hotunan ne a yayin da ake yin liyafar cin abincin rana wacce aka shirya domin bikin Yusuf Buhari
  • An yi liyafar a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa ta Aso Villa a ranar Lahadi, 22 ga watan Augusta

Aso Villa, Abuja - Kyawawan hotunan 'ya'ya matan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Halima, Zahra da Hanan tare da mazansu na aure yayin liyafar cin abincin rana ta bikin dan uwansu, Yusuf Muhammadu Buhari sun bayyana.

An yi kasaitacciyar liyafar, wacce ta hada manyan mutane a ranar Lahadi, 22 ga watan Augusta a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa ta Aso Villa.

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure
Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure. Hotuna daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

'Ya'yan shugaban kasan mata sun karkace tare da daukar kyawawan hotuna da mazansu na aure yayin da ake liyafar cin abincin ranan.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya gayyaci Mufti Menk domin walima ta musamman

An ga Halima Muhammadu Buhari tare da maigidanta, Mohammed Sheriff

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure
Halima Buhari da mijinta, Mohammed Sheriff. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Ba a bar 'yar kwalisa Zahra Muhammadu Buhari a baya ba, hoton ta ya bayyana tare da maigidanta Ahmed Indimi a wurin liyafar.

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure
Zahra Buhari tare da mijinta Ahmed Indimi. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Aisha Hanan Buhari da kanta ta dauka kyakyawan hoto tare da mijinta Muhammad Turad Sha'aban a wurin liyafar.

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure
Hanan Buhari da mijinta Muhammad Turad Sha'aban. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Asali: Legit.ng

Online view pixel