Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari

Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari

  • Buhari yace ba zai yiwu ya bar mulki a matsayin wanda ya gaza ba
  • Shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin tsaro a ranar Alhamis
  • Buhari ya yi farin ciki bisa nasarorin da ake samu kan yan ta'addan Boko Haram

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya lashi takobin cewa ba zai yiwu ya bar mulki a kunyace ba idan ya karashe wa'adinsa na biyu a shekarar 2023.

Ya bayyana hakan yayin zaman majalisar tsaro tare hafsoshin tsaro ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja, rahoton ChannelsTV.

Mai bada shawara kan lamarin tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Munguno, ya mika sakon Buhari ga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen ganawar da aka kwashi sa'o'i biyar ana yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

Yace:

"An yiwa shugaban kasa bayani, kuma ya ji dadi sosai ganin idan dimbin nasarorin da aka samu musamman bayan nadin sabbin hafsoshin tsaro da Sifeto Janar na yan sanda."
"Kuma ya bayyana cewa bai shirya barin gwamnati a kunyace ba; ba zai yarda hakan ya faru ba."

Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari
Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari
Asali: Instagram

An samu nasarar da ba'a taba samu ba

Munguno ya kara da cewa abubuwan da suka tattauna akai shine nasarorin da ake samu a faggen yaki a Arewa maso gabas.

Yace:

"Dimbin mutane a Arewa maso gabas dake mika wuya na nuna kokari da jajircewan Sojoji, jami'an leken asiri da sauran jami'an tsaro."
"Bamu taba ganin irin wannan adadin mutane suna mika wuya ba, hasali hakan na faruwa ne saboda ire-iren abubuwan dake faruwa a faggen dama, lamarin fadace-fadace tsakanin bangarorin yan ta'addan."

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng